✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Mun rika cin ciyawa lokacin da muke hannun Boko Haram’

Wata matar aure mai shekara 25 kuma mahaifiyar ’ya’ya biyar mai suna A’isha Bukar ta bayyana irin kuncin da suka shiga a lokacin da suke…

Wata matar aure mai shekara 25 kuma mahaifiyar ’ya’ya biyar mai suna A’isha Bukar ta bayyana irin kuncin da suka shiga a lokacin da suke hannun mayakan Boko Haram, inda ta ce, ita da mijinta da surukarta da ’ya’yansu sun rika cin ciyawa ce domin su rayu.

A’isha Bukar wadda take daya daga cikin wadanda Boko Haram ta sace ta kubuta ne daga hannunsu lokacin da jirgin yakin sojojin sama ya rika ruwan bama-bamai a maboyarsu a dajin Sambisa a kwanan nan.

Ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a ranar Litinin da ta gabata cewa, sun gudo ne tare da mijinta da surkarta da kuma ’ya’yansu biyar. Ta ce ’yan ta’addan sun tsare iyalansu na kimanin shekara uku a dajin Sambisa bayan sun kama su a gonarsu a kauyen Talala da ke karamar Hukumar Dambuwa a Jihar Borno.

A’isha Bukar ta ce ’yan Boko Haram din sun hana su abinci da magani ne saboda mijinta ya ki shiga sojinsu. “Muna cikin aiki a gonarmu ’yan ta’addan suka sace mu ni da mijina da ’ya’yanmu da kuma surukata. Sun dauke mu zuwa can cikin dajin Sambisa, inda muka zauna na kimanin shekara uku,” inji ta.

Ta kara da cewa: “Sun bukaci mijina ya dauki makami ya yi yaki tare da su, bukatar da ya ki; sai suka fusata suka kira shi da mai taurin kai; kuma domin su tankwara shi, sai suka hana mu abinci da magunguna. Mun rika rayuwa kan cin ganyayyaki da ciyayi; kuma mun dogara ne da itatuwa wajen yin magunguna idan ba mu da lafiya; sukan raba abinci ne kawai ga mayakansu da wadanda suka mika wuya ga bukatunsu.”

A’isha Bukar ta koka kan yadda ’yan ta’addan suke gallaza wa jama’a da tozarta mata da kananan yara da suka kama.

Wadda ta kubutar ta ce, ’yan ta’addan sukan tilasta wadanda suka kamo ciki har da mata da yara su rika halartar wa’azi da laccocinsu. Ta ce: “An rika dukan mijina a lokuta da dama saboda rashin halartar wuraren laccar. Bayansa duk ya yi tabo saboda raunikan da ya samu saboda dukan rashin tausayin da ’yan ta’addan suke yi masa.”