Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Mun sanya aikin gyaran hanyar Jos zuwa Kaduna a kasafin kudin bana – Maitala Jingir

Alhaji Haruna Maitala jingir

Mun sanya aikin gyaran hanyar Jos zuwa Kaduna a kasafin kudin bana – Maitala Jingir

Dan Majalisa Wakilai mai wakiltar mazabar Jos ta Arewa da Bassa da ke Jihar Filato Alhaji Haruna Maitala Jingir ya ce an sanya aikin gyara hanyar Jos zuwa Kaduna a kasafin kudin bana.

Alhaji Haruna Maitala Jingir ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi a wajen taron Ranar Kabilar Jere da aka gudanar a garin Jingir a ranar Asabar da ta gabata.

Ya ce ganin irin wahalar da matafiya suke sha a kan hanyar sakamakon lalacewar da ta yi shekara da shekaru ya sa suka tsaya tare da taimakon Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai Alhaji Ahmed Maje da Gwamnan Jihar Filato, Barista Simon Lalong wajen ganin an sanya aikin hanyar a kasafin kudin bana.

Ya ce abin da rage yanzu shi ne za su tsaya wajen ganin an samu kudin da za a zo a fara aikin gyaran hanyar.

Ya bai wa al’ummar mazabarsa tabbacin cewa nan bada dadewa ba, zai bi dukkan al’ummar mazabar ya bayyana musu irin ayyukan da suka sanya a gaba a  mazabar.

“Dangane da cibiyar koyar da sana’o’i da kungiyar al’ummar kabilar Jere suke son kafawa, don koya wa matasa sana’o’i zan kasance daya daga cikin wadanda za su yi aikin gina cibiyar,  har a kammala aikin.Don haka ina kira ga al’ummar Jere mu ci gaba da zaman lafiya, kamar yadda aka sanmu domin babu wani ci gaba da za a samu, idan babu zaman lafiya,” inji shi.

Babban Bako Mai Jawabi, kuma malami a Kwalegin Ilimi ta Tarayya da ke garin Panshin, Mista Auwalu Gimi ya yi kira ga ’yan kabilar Jere su yi kokari su rika tallafa wa ’ya’ya mata, suna tafiya makarantu, maimakon takura musu su yi aure da wuri.

Ya ce babu shakka akwai matsalar rashin tura ’ya’ya mata zuwa makarantu, a kabilar ta Jere. Don haka ya ce ya zama wajibi kabilar su canja wannan hali su rika karfafa wa ’ya’ya mata gwiwa, suna tura su makarantu domin a samu ci gaba a kabilar da kasa baki daya.

A jawabin Garkuwar al’ummar Hausa Fulani na yankin Pengana, Alhaji Ya’u Bala Jingir ya ce ya kamata a karrama al’ummar yankin  Pengana kan zaman lafiyar da suke da shi a yankin.

Ya ce suna da kabilu sama da 20, amma duk rikice-rikicen da aka samu a Jihar Filato a shekarun baya ba a taba samun tashin wani hankali a yankin ba.

Tun farko a jawabin Shugaban Kungiyar Al’ummar Jere na Kasa Mista Ibrahim Chukuri ya ce babban dalilin da ya  sanya suke shirya wannan taro a kowace shekara shi ne domin su bunkasa al’adunsu na kabilar Jere tare da tattauna matsalolin da suke damunsu domin  a dauki matakan magance su.