Search
Subscribe
Mun shiga firgici bayan sace dalibai da malamansu a kauyenmu – Mutanen Kakau Daji

Makarantar Engravars da aka sace dalibai da malamansu a kauyen Kakau Daji a Jihar Kaduna

Mun shiga firgici bayan sace dalibai da malamansu a kauyenmu – Mutanen Kakau Daji

Al’ummar kauyan Kakau Daji a Karamar Hukumar Chikun da ke Jihar Kaduna sun ce suna cikin damuwa kan rashin tsaro a yankin tun kafin a sace dalibai mata shida da malamansu biyu a wata makaranta da ke kauyen da masu garkuwa da mutane suka yi a makon jiya.

Masu garkuwa da mutanen sun yi wa wata makarantar kwana mai suna Engrabars da ke kauyen dirar mikiya da misalin karfe 12:10 na dare rike da miyagun makamai inda suka sace su.

Daliban da aka sace masu shekara 16 zuwa 18, wadanda suka sace su, sun bukaci a ba su miliyoyin Naira inda suka yanke Naira miliyan 10 kan kowace daliba da malami a matsayin fansa, kuma har zuwa hada wannan rahoto ana ci gaba da ciniki kan yadda za a kubutar da su.

Wakilinmu wanda ya ziyarci kauyan ya ruwaito cewa makarantar duk da cewa ta kwana ce tana da girma da ajujuwa sannan babu gidaje da yawa kusa da ita.

Ya bayyana cewa a lokacin ziyararsa babu ko dalibi a makarantar saboda iyayen daliban sun kwash esu don gudun kada a yi musu tsakiyar da babu ruwa a sake dawowa a sace sauran daliban.

Duk da cewa makarantar na kiwaye da katanga amma katangar ba ta da tsawo wanda hakan ne ya bai wa barayin mutanen damar shiga cikin makarantar cikin sauki.

Bayanai sun ce barayin mutanen sun shiga makarantar ce bayan sun bi ta gifen da ake ajiye janareta wanda ba a katange ba kafin su wuce kai-tsaye zuwa sashen malaman makarantar.

Aminiya ta zanta da wadansu mazauna kauyen Kakau Daji da ke kusa da makarantar kan halin da suke ciki bayan aukuwar lamarin.

Akasarinsu sun nuna suna tsoron yin magana da ’yan jarida amma daya daga cikinsu mai suna Habi ya ce a yanzu harkar rashin tsaron ýta dagula musu hankali a kauyen baki daya.Ya ce yanzu haka mazauna yankin ba su iya kiwo a gidajensu duk da cewa a kauye suke. Ya ce hatta noma suna yi ne kurum amma babu  kwanciyar hankali.

“Tun kafin aukuwar harin da aka kai makarantar ’yan matan nan dama muna fama da rashin tsaro a yankin. A yanzu kauyen da dan mutane kuma a halin da muke ciki a yanzu shi ne jami’an tsaro na dan shiga ciki su dan yi zagayensu su fice ba kamar da ba da ba a ganinsu ba.

Batun noma kuwa a yanzu dai jama’a na tsoron shiga daji. Hakan ya sa ba ma iya yin noma yadda ya kamata, a bana ba mu yi noma sosai ba. ’Yan kadan ne ke kokarin zuwa gona da ke nesa da gida,” inji Habiý.

Ya kara da cewa: “Muna kira ga gwamnati ta samar mana da karin jami’an tsaro domin hakan zai taimaka wajen ba mu kwarin gwiwar zuwa gona. Ka ga a yanzu mu talakawa tunda ba mu yin noma sai ka ga ’ya’yanmu a yashe a gida ba su zuwa makaranta domin sai mun yi noma za mu samu dan abin da za mu tura yara makaranta. Idan jami’an tsaro na kaiwa da komowa a garin mutane za su ci gaba da harkokinsu cikin kwanciyar hankali. Amma a yanzu abubuwa babu dadi. Akasarin mutanenmu manoma ne sai matasamu masu shiga cikin gari su yi kwadago. Amma yawancinmu noma muke yi da kiwo, yanzu wadannan barayi sun hana mu kiwo. Da za ka ga muna ajiye dabbobi a gidajenmu amma tunda muka ga an fara sace mutane da dabbobi duk mun bari.”

Wani mai suna Johný ya shaida wa wakilinmu cewa su da suke bin wannan hanya da ta bi ta gaban makarantar suna taka-tsantsan saboda rashin tsaro a cikin dajin.Ya ce tun kafin a sace ’yan matan a makarantar akwai matsalar tsaro a yankin. Domin akan sace mutane tare da yin garkuwa da su a dajin.

“Idan yamma ta yi, in ba dole ba gaskiya ba mu son bin wannan hanya domin da wuya ka ga gari kusa saboda makarantar cikin daji take kuma kusan tafiyar minti 20 zuwa 30 ne daga bakin titin Kakau zuwa makarantar. Sannan akwai matsalar tsaro dama can a yankin namu tun kafin wannan abu ya faru a makarantar. Don haka muna cikin damuwa wanda hakan ya sa iyayen yara suka kwashe ’ya’yansu daga makarantar,” inji shi.

Wani da ya ki ambatar sunansa ya ce maharan sun yi wa ma’aikatan makarantar duka da itace kafin su wuce dakunan kwanan dalibai ’yan mata. Daliban ba su da masaniyar abin da ke faruwa sai da mutanen suka dira dakinsu suka bukaci matar da ke kula da su ta nuna musu wadanda iyayensu ke da hali, inda ta ce ba ta sani ba. Daga nan ne sai suka shiga tsinta da kansu,” inji shi.

A yanzu makarantar babu kowa sai Shugaban Makarantar da wadansu malamai biyu da wakilinmu ya gani a cikin makarantar. Da farko sun ki yin magana amma daga baya Shugaban Makarantar Mista Shunom Giwa ya yi wa Aminiya bayani a takaice kan yadda lamarin ya auku.

Ya ce yana cikin barci da misalin karfe 12:10 sai ya ji motsi a harabar makarantar wanda bai saba jin irinsa ba, da ya fahimci barayi mutane ne suka shiga masu makarantar sai ya umarci matarsa da ’ya’yansa su shiga cikin uwar daka.

“Suna cikin kokarin balle kofar sai na ce su bari zan bude. Da na bude musu sai na ga mutum biyar matasa da makamai, suka bukaci in kwanta a kasa, na kwanta. Suka ce in ba su abin da nake da shi a aljihuna, na ba su. Sai suka yi kokarin shiga cikin uwar dakin sai na mike domin kawar da da hankalinsu amma sai suka sake cewa in kwanta. Can sai  naga an taho da abokin aikina suka ce ya kwanta a kasa da na lura hankalinsu na kan abokin aikina sai na ruga cikin daji suka yi harbi amma Allah Ya sa ba su same ni ba. Tunaninsu ina cikin wancan ajin ne suka dudduba ba su gan ni ba. Da ba su gan ni ba ne suka fara neman inda dakunan dalibai suke. Ni kuma sai na fara tunanin mai zan yi. Sai kurum na soma ihu ina cewa ‘ihu ’yan banga, ihu ’yan sanda ga masu garkuwa da mutane,” inji shi.

Ya ce jin haka “Sai suka fara harbi ta inda nake sai na gudu na tsallake katangar na fice daga makarantarý. Ina can a fake har sai da na soma jin kukan karnuka sai na fahimci su ne ke shirin tafiya. Daga nan sai na ji muryar abokin aikina yana kiran sunan daya daga cikin shugabannin daliban. Da ya amsa sai na fito daga inda nake boye.”

Ya ce daga nan suka fara kirga dalibansu domin sanin wadanda ba su nan, a nan ne suka fahimci sun tafi da daya daga cikin shugabannin makarantar mai suna Joel Adamu da Shugabar Dakin Kwanan Daliban da dalibai mata shida.

Mista Shunom ya ce makarantar na da dalibai kusan 100 amma a kullum raguwa suke yi saboda rashin tsaro domin iyayen yara suna cire su daga makarantar tun kafin aukuwar haka.

“Yanzu haka masu garkuwa da mutanen sun tuntube mu kuma muna tattaunawa da su kan yadda za a sako daliban da malamansu. Saboda ihun da na rika yi ne ya sa suka yi saurin ficewa daga makarantar in ba haka ba da za su iya tafiya da dukkan daliban,” inji shi.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin