✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun shigo Azumin watan Ramadan

Dukkan dangin yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah ubangijin halittu tsiranSa da AmincinSa su kara tabbata ga fiyayyan halitta Manzon tsira Annabi…

Mai Alfarma Sarkin Musulmi , Alhaji Muhammad Sa’ad AbubakarDukkan dangin yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah ubangijin halittu tsiranSa da AmincinSa su kara tabbata ga fiyayyan halitta Manzon tsira Annabi Muhammad Sallalahu Alaihi Wasallam, da alayansa Ale Akilu da Ale Abbas da Ale Jafar da Ale Aliyu da sahabbansa wadanda su ne suka yi mana tsuwurwurin wannan addini har ya kawo garemu, Allah ya yarda da su baki daya, da kuma wadanda suka bi tafarkinSa har ya zuwa ranar sakamako. Ina shaida wa babu abin bautawa bisa cancanta da gaskiya sai Allah kuma Annabi Muhammad bawanSa ne kuma manzonSa ne, dukkan wanda Allah ya shiryar shi ne hakikanin shiryayye, dukkan wanda Allah ya batar babu mai iya shiryar da shi.
Ya ‘yan uwa kamar yadda muka sani lokaci na kara turawa gaba, mun shigowata mai alfarma wato Ramadan. Kuma ga mai hankali yasan da cewa kwanakinmu muke cinyewa a hankali, lokutanmu ne suke tafiya, hakika dukkan lokacin da ya tafi to ya riga ya shiga kundin tarihi, lallai mun kasance al’umma masu hasarar lokutanmu masu tsadar gaske ba mu sani ba ko kuma muna gafale, kamar yadda Allah yake fada a cikin sura ta 2 aya ta 164 an sanya dare da rana masu shudewa, wanda yake nuna mana cewa wucewar dare da rana alama ce ta tafiyar lokaci a garemu, kuma muna kara kusa ga ajalinmu ne bamu sani ba, muna ta addu’a “Allahumma Balligna Ramadan” amma kuma muna kara kusanta kanmu ya zuwa ga ajalinmu ne ashe. Lallai lokaci abu ne mai tsadar gaske a cikin rayuwarmu, a saboda muhimmancin lokaci ne Allah ta’ala da kansa ya yi rantsuwa da lokaci a cikin sura ta 103 dan ya nuna mana muhimmancinSa subhanahu wata’ala, tsarki ya tabbata a gareshi.
Ya ‘yan uwana, kamar yadda Allah ya ba mu labari acikin Alkur’ani mai tsarki; wannan
wata da yake tun karomu na Ramadan shi ne watan alkurani kamar yadda Allah ya shaida mana a cikin sura ta 2 aya ta 185, Allah ta’ala da kanSa ya yi kira a garemu cikin wannan aya da cewa duk wanda ya halarci wannan wata ma’ana duk wanda ya
riski kansa a wannan lokaci to ya azumceshi. Haka kuma har ila yau Allah ya ci gaba da shaida mana acikin wannan sura aya ta 183 cewa shi wannan wata kwanaki ne kididdigaggu, kamar Allah yana cewa ne mu yi amfani da lokutanmu ta hanyoyin da suka dace a cikin wannan wata.
Ya ‘yan uwa masu girma, kamar yadda muka sani, mun bata tare da hasarar lokuta masu yawa muna barci da da shagaltuwa da wasu abubuwa wadanda ban a larura ba a kusan watanni 11 da suka gabata. To lallai yana da kyau a wannan watan mu yi dukkan mai yuwuwa wajen ganin mun ribaci wannan lokaci. Wannan wata na Ramadana kamar yadda malamai suke ta bayani yana daga cikin watanni masu dimbin falala kuma kwanakinsa guda 29 idan ya yi tsawo ya cika kwana 30, darensa da wuninsa duka cike suke da dimbin falala, kamar yadda ya zo a cikin ingatattun hadisai cewa ana bude dukkan kofofin alkhairi a wannan watan haka kuma ana kulle dukkan kofofin sharri a wannan watan. Haka kuma a cikin wannan wata ne ake da dare guda, wanda ya dara watanni dubu alkhairi (lailatul kadri). Kamar yadda muka sani wannan watan yana da makonni hudu da kwanaki 29, a cikin kowace rana akwai sa’o’i 24, haka kuma a cikin kowace sa’a muna da dakika 60, don haka idan muka hada lissafi muna da sa’o’i 696 a cikin wannan wata, lallai akwai bukatar mu tsaya mu kalli wadannan sa’o’i mu tsara lokutanmu da kuma kokarin kiyaye ka’idar da muka sanya wa kawunanmu.
Sau da yawa wasu daga cikinmu sukan dauka watan azumi lokaci ne na aci kayan dadi a more kawai. Lallai akwai bukatar mu ci daga cikin abin da Allah ya hore mana, amma kuma mu zage damtse wajen yin ibada karatun Alkur’ani dare da rana safe da yamma, zikirin safe da na yamma, sallolin farilla cikin jam’I da kuma sallolin Nafila da kiyamullaili. Idan aka ce maka watan Ramadan ya kama a farko-farko idan kaje masallatanmu abin gwanin ban sha’awa domin duk masallacin da kaje zaka ga ya cika da jama’a wani zubin mutane har a waje suke sallah, masallacin da ake yin sahu biyu a sallar asuba sai ka tarar ya cika makil a farkon Ramadan; amma daga zarar ance maka an tsallake goman farko, sai ka fara ganin karancin mutane a masallatai, da guraren karatuttuka.
Haka kuma, a cikin sahihin hadisi Manzon Allah yana cewa ku fanshi kanku daga wuta ko da da barin dabino ne. lallai wannan babbar magana ce, muyi kokari wajen yawan aikata alkhairi da ciyarwa a wannan watan gwargwadon hali, idan kana da ikon sayan dabino na Naira goma yi gaggawa ka saya, domin ka fanshi kanka kamar yadda manzon Allah ya fada (salallahu Alaihi Wasallam). Lallai hanyoyin amfani da lokuta a wannan wata suna da yawa, kamar yadda nasan ‘yan uwana da suke gabatar da shirye-shirye a filaye daban daban za su yi bayani, mai gamsarwa.
Aminu dankaduna Amanawa,  ya rubuto daga sokoto.
Za ku iya samunsa ta wadannan hanyoyi. 07065654787./ 08180649578. Ko ta imel. [email protected]