✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun shirya gasar kwallo ne don karfafa zumunci da kaunar juna – Alhaji Baballiya

Ko’odinetan gasar kwallon kafa na Lali Super Ten da ake bugawa a Kafanchan da ke Kudancin Kaduna, Alhaji Baballiya Musa ya bayyana cewa sun shirya…

Ko’odinetan gasar kwallon kafa na Lali Super Ten da ake bugawa a Kafanchan da ke Kudancin Kaduna, Alhaji Baballiya Musa ya bayyana cewa sun shirya gasar kwallon kafa tsakanin kulob-kulob din kwallo na cikin garin Kafanchan da takwarorinsu na kewayen garin ne don kara karfafa zaman lumana da ya samu a yankin.

Baballiya, ya bayyana wa Aminiya haka ne a filin wasan kwallon kafa na garin Kafanchan yayin ci gaba da buga wasannin da ake yi wanda wani matashi dan yankin, Ibrahim Shu’aibu da ke buga wasa a kasar Norway ya dauki nauyin shiryawa.

“Saboda kishin garinsa da kuma kaunar ganin an samu hadin kai da zaman lafiya ta hanyar kwallon kafa, ya sa wannan dan wasa ya shirya wannan gasa wadda cikin kulob goma da ke cikin gasar, uku ne kawai na Musulmi da suka fito daga cikin garin Kafanchan yayin da sauran na Kiristoci ne da suka fito daga kewayen garin Kafanchan, kuma kowane kulob idan ka duba ba za ka rasa Musulmi da Kirista a ciki ba ko da ba yawa,” inji shi

Ya bayyana wanda ya shirya  gasar a matsayin mutum na farko da ya taba shirya gasar da ya dauki nauyin komai da kansa, kama da yi wa kowace kungiya rajista kyauta zuwa saya wa kowane kulob setin kayan wasa kyauta da aka kiyasta kayan kowane kulob kan Naira dubu 45 zuwa dubu 50.

“Sannan ga kyaututtuka masu gwabi da ya tanadar wa wadanda suka yi kwazo a gasar a matakai daban-daban,” inji shi.

“A karon farko da na biyu da aka shirya gasar an gudanar da ita ce a tsakanin kulob-kulob din cikin gari a tsakanin layukan da ke garin Kafanchan. Amma a wannan karon da shi ne na uku an fadada abin zuwa unguwannin kewayen garin don sanya sauran kabilun a ciki,” inji shi.

Ya ce suna sa ran wasa na gaba za a gudanar da shi ne a tsakanin dukanin gundumomi 12 na Karamar Hukumar Jama’a yayin da gasar shekara ta 2020 kuma za su gayyato dukan kananan hukumomi takwas na yankin Kudancin Kaduna.

Da yake tofa albarkacin bakinsa, wani dan wasa, wanda kuma shi ne ya fara horar da dan wasan da ya shirya gasar, Aminu Ibrahim ya yi kira ne ga ’yan sanda da sojoji su yi koyi da wannan dan wasan wajen shirya irin wadannan wasanni tsakanin matasan yankin mabiya addinai da kuma kabilu daban-daban don kara dunkulewa wanda yin hakan, a ganinsa, zai taimaka musu wajen ayyukan wanzar da zaman lafiya a yankin.

“Ba lallai aikinsu ya zama sai ana tashin hankali ba. Akwai ayyukan da ake bukata yayin da ake zaman lafiya don dauke hankalin jama’a da kawar da tunani daga fadace-fadace,” inji shi.

Aminu, wanda tsohon mai tsaron baya ne a kulob din JCR Riders da ke Jos, Jihar Filato da kuma UNICEF Robers da ke Kalaba, Jihar Kuros Riba, ya ce kudin da mai shirya gasar ya kashe shi kadai ba kungiya ko gwamnati ko dan siyasa abin a yaba ne.

“An saba yawancin lokuta idan ana rikici a Jihar Kaduna to garin Kafanchan na cikin dar-dar ne amma wannan karon sai ga shi ana rikici a Kasuwar Magani da Kaduna amma nan muna cakude Musulmi da Kirista a filin kwallo ana wasa cikin kwanciyar hankali,” inji shi.

Wanda ya shirya gasar, Ibrahim Shu’aibu Lali, ya fara zuwa buga wasa a CSKA Moscow ne a kasar Rasha kafin ya koma FC Haugesaund ta kasar Norway inda su kuma suka bayar da aronsa ga kulob din Kongsbinger FC inda ya kammala wasansa a bana zai kuma koma kulob din sa na FC Haugesaund, bayan kafa tarihin cin kwallaye 17 da ba a taba samu a kulob din na Kongsbinger ba kuma ya samu nasarar farfado da su.

Kulob-kulob din da suka shiga gasar sun hada da Police Academic FC da Jama’a Emirate FC da Golden Balley FC da dukansu suka fito daga cikin garin Kafanchan, sai sauran da suka hada da Kaninkon FC  da Garaje Bombers da Ungwan Masara FC da Katsit FC da Bayan Loko FC da Aduan FC da Takau FC.