✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Mun shirya magance rashin bin doka a kan hanyoyin Najeriya’

Dalilai da dama ciki har da mugun gudu da tuki cikin maye da rashin bin layi da sauransu suna daga cikin abubuwan da suke kawo…

Dalilai da dama ciki har da mugun gudu da tuki cikin maye da rashin bin layi da sauransu suna daga cikin abubuwan da suke kawo hadarurruka a kan hanyoyin Najeriya. Duk da cewa akwai mutane da dama da suke wasa da batun daukar rashin bin layi da muhimmanci, hakan na daya daga cikin manyan abubuwan da suke kashe ’yan Najeriya a kan hanyoyi.
Tun lokacin da gwamnatin soja ta Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya kafa Hukumar Kiyaye Haddura ta kasa (FRSC) a 1988, hukumar ki aiki gadan-gadan domin rage hadarurruka a kasar nan. Kuma duk da wannan babban kalubale, Hukumar FRSC ta yi kokari sosai a kokarinta na samun nasara.
Rashin bin layin da ya dace rashin bin dokar tuki ne, musamman a abin da ya shafi kiyaye layukan. Galibi akan samu matsalar rashin da’a idan direbobi suka koma hagun na layin dama. Kuma an lura lokacin bukukuwa kamar na Sallah da Kirsimeti da Sabuwar Shekara sun fi zama mafiya kalubale ga ma’aikatan Hukumar FRSC saboda da gangan direbobi suke karya dokokin tuki.
Da take tattaunawa da Aminiya kan kalubalen rashin bin ka’ida a kan titunan kasar nan Kakakin Hukumar FRSC, Stella Uchegbu ta ce: “Rashin bin layin da ya dace a kan hanyoyi yana taimakawa wajen aukuwar hadarurrukan da za a iya kauce musu. Kuma yana jawo keta dokokin tuki inda irin wannan mugun hali na masu tuki a galibi shi ke haifar da hadari a kan hanyoyin. Rashin tarbiyyar tsayawa kan layi kan jawo miyagun raunuka ga direba da fasinjoji da ke cikin mota tare kuma da yiwuwar lalata dukiya (mota). Don haka a Hukumar FRSC, rashin bin layi a kan hanya babban kalubale ne, musammam ganin rayuwar da yake ci. Abubuwa da dama da suka hada da rashin da’a wajen bin layi ke jawo hadarurruka a hanyoyin Najeriya. Kuma sananne ne cewa dan Adam ke jawo kimanin kashi 90 cikin 100 na hadarurrukan da suke faruwa a hanyoyinmu. Kuma direbobi ne suke haifar da mafi yawan kalubalen. Kuma saboda illar da rashin bin layin da ya kamata da diribobi ke yi, Sashi na 161 (3) na Dokokin Tuki a Hanyoyi na kasa na 2012 ya ce: “Direban mota da ke kan hanyar da jama’a ke amfani da ita da layi da ke nuna wasu alamu na ka’idojin tuki ya raba ta, ba zai bar wani layi zuwa wani ba, sai ya tabbatar wajen yin hakan ba zai jawo matsala ko jefa rayuwar sauran masu amfani da hanyar ba.”
Saboda damuwa da halayen wasu direbobi a hanyoyin Najeriya, Uchegbu ta kara da cewa, “A matsayin hukumarsu ta jagoran hukumomin kare haddura da kula da tsare dokokin tuki, sun samu gogewa, saboda a kokarin da take yin a sauke nauyin da aka dora mata, dan Adam ne ya fi jawo hadari.  dauki misali da Abuja, wadda take takama da ingantattun hanyoyi da kwarewa wajen kula da kai-kawon ababen hawa, ga na’urorin bayar da hannu masu aiki da alamun kan hanyoyi da sauransu, duk da haka Abuja ce ta fi samun hadarin mota a kan hanyoyinta, hakan na nuna cewa duk da kyan hanyoyin, hadarurrukan suna karuwa ne. Don haka babban abin da muka fi mayar da hankali shi ne dabi’u da halayen masu amfani da hanyoyin.”
Shi kuwa Sufeto Jubril M. Ibrahim na hukumar da ke bayyana irin abin da ya gani game da bin layi a kan hanya ya ce, direbobi da dama ba su bin doka kuma suna da matukar gajen hakuri. “Mutanen Najeriya ba su girmama doka, kuma suna da gajen hakuri. Abin bakin ciki, maimakon su yi abin da ya dac, sai su rika tunanin jami’an tsaro suna keta musu hakkokinsu ne. Babban kalubalenmu shi ne jami’an tsaro da ke tuki a hanya mai falle daya a duk lokacin da aka samu tsaikon ababen hawa. Sukan yi tawaye wa duk wani yunkuri da za a yi don su bi ka’ida,” inji shi.
Game da adadin keta dokar bin layi a tituna a kullum ya ce, “Suna da yawa. Abu ne mai wahala a bayar da adadi.”
A mahadar titin Dutsen-Alhaji da ke yankin Bwari a Birnin Tarayya Abuja, wakilinmu ya iske ana cacar baki a tsakanin wani babban dan sanda da ke aikin kula da ababen hawa a Ltinin din makon jiya (da safe) da kuma wani babban jami’in soja. Sojan wanda ke tuka wata dafa-duka mai launin ja dauke da lambar Abuja: Kuj 524 GT ya bi hanyar da ba tasa ba ce a kokarinsa na kauce wa jerib gwanon motoci da ke gefen da ya kamata ya bi. dan sandan ya gaya masa cewa: “Dukkanmu ma’aikatab sarki ne; bai kamata ka kalubalance ni a bainar jama’a ba. Ya kamata ka yi min magana cikin girmamawa.”
Wani babban jami’in ’yan sanda ma ya fadi kan yadda ake karya dokar bin layi cewa: “Mutanen Najeriya ba su da da’a, sabanin yadda lamarin yake a sauran kasashe. Galibi dan Najeriya ’yan kamar ’yan banga ne. Sukan karya doka duk lokacin da suka so. Wannan ne ya sa galibi suke nuna rashin da’a wajen bin  layi a yayin tuki ba tare da lura da mugun illar da ke cikin haka ba. Kuma mafi muni, jami’an tsaro ne suka fi zama barazana kan tafiyar tsabta a ka hanya. Sun yin imanin cewa suna da ikon karya dokokin hanya.”
A kan titin Gado Nasko da ke rukunin gidaje na Federal Housing a Kubwa da ke yankin Bwari, wakilinmu ya lura da yadda matuka motoci da dama suke gaza bin layi daya, musamman a lokacin da aka samu cinkoson ababen hawa da yamma. Sukan wuce abokin tafiy tare da jefa rayuwar sauran masu bin titi a cikin hadari.
A shataletalen Sokale da ke Dutse, wakilinmu ya lura da yadda masu amfani da hanya musamman ’yan acaba suke yawan keta dokar bin layi, da damansu suna bin hannun da ba nasu ba.
Wani direban taksi a Mabushi da ke birnin Abuja da ya bayyana sunansa da Richard ya shaida wa Aminiya abin da ke sa masu motoci ke nuna rashin da’a wajen kauce wa bin layi inda ya ce: “Mutanen Najeriya suna da al’adar mugun tuki. Lokuta da dama nakan ji takaici kan yadda da damarmu muke tuki. Muna tuki ne kamar wasu gaulaye. Babbar matsala ce da Hukumar Kiyaye Haddura ta kasa ya kamata ta magance ta. Akwai bukatar a rika fadakarwa. Kuma wani abin takaici shi ne wadanda suke kafa dokokin ba su mutunta su. Akwai bukatar a yi wani abu, babu shakka jami’an Hukumar FRSC suna aiki mai kyau, amma akwai bukatar su ninka kokarin da suke yi.”
Wani direban taksi mai suna Bartholomew Saleh kuwa cewa ya yi: “Bari in gaya maka, galibinmu ba mu aiki da kwakwalwarmu lokacin da muke tuki. Ba mu tunani yadda ya kamata, kuma muna rikon sakainar kasha wa al’amura ciki har da batun tsaro. Kuma ’yan Najeriya koyaushe cikin gaggawa suke. Kuma abin da ya fi muni, irin wadannan mutane sukan rika sheka gudun da bai kamata ba. Sannan bayyanar sababbin motoci da ke iya tafiyar kilomita 60 cikin ’yan mintoci, sai lamarin ya dada zama hadari. Muna da miyagun halaye a kasar nan.”
A makon jiya ne kafafen watsa labarai suka bayar da labarin yadda Gwamnan Jihar Legas Babatunde Fashola “ya kamata” tare da hana wasu jami’an soja biyu tuka motocinsu a layin da aka ware wa motocin bas-bas (BRT) a Outer Marina da ke yankin Island. A fili rashin bin layi ne hafsoshin sojan suka yi. Gwamna ya nuna kaduwa kan yadda wadanda ya kamata su tabbatar da ana bin doka su ne suke karya ta.
Matakin da Gwamnan ya dauka an ce ya jawo hankali tare da samun yabo daga masu motoci da sauran masu wucewa wadanda suka rika kwarara masa yabo kan nuna kyakkyawan shugabanci.
Da yake kara bayani a kan lamarin Gwamna Fashola ya ce: “Ba zan lamunci karya doka ba. Kuma za mu dauki alhakin kula da zirga-zirga a kan hanyoyinmu. Ba na amfani da layin bas-bas, nakan bin layin motoci, kuma ina fata duk wanda zai tuka motarsa ya yi haka.”
Da yake kara haske kan yadda Hukumar FRSC ke kokarin magance rashin da’a wajen bin layi, kakakin hukumar ya ce: “A kowace rana muna nazari kan yadda ake tafiya kan hanyoyi da kuma bullo da dabarun magance su. A lokacin taron shugabanninmu na mako-mako mukan karbi rahotanni daga sassa daban-daban na kasar nan, kuma mukan yi amfani da bayanan da muke da su kan hadarurruka a kan hanyoyi ko karya dokokin hanya da masu aikata laifuffukan. Kuma akwai wasu dabaru nan emo hanyar magance wannan matsala. Har wa yau muna ci gaba da jawo jama’a a harkar ta hanyar shirya gangami a tashoshin mota, da kamfe din jerin gwanon motoci da ziyarar bayar da shawara ga wadanda lamarin ya shafa da amfani da kafafen watsa labarai wajen bayar da shawarwari da hada hannu da masu ruwa da tsaki da kuma tabbatar da ana bin dokoki da ka’idojin tuki. A matsayin hukumar da take da wayewa mun dogara wajen tsoma jama’a a lamarin domin cimma nasarorin da aka tanada.”
Ya karkare da cewa: “Domin magance batun rashin bin doka kan layi da direbobi ke yi muna kara daukar matakan kamawa da hukunta masu karya doka. Kuma muna aiki wurjanjan; kuma mun kudiri aniyar cimma nasarar kawo tsabta a kan hanyoyin Najeriya.”