✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun yi gudun gara a Najeriya muka tarar da zago a Libiya – ’Yan Najeriya

A yammacin ranar Alhamis din makon jiya ne karin mutum 141 suka sauka a filin jiragen sama na Murtala Mohammed da ke Legas a wani…

A yammacin ranar Alhamis din makon jiya ne karin mutum 141 suka sauka a filin jiragen sama na Murtala Mohammed da ke Legas a wani bangare na yunkuri da mahukuntan kasar nan ke yi don dawo da ’yan Najeriya da suka samu kansu a mawuyacin hali a kasar Libiya.

Aminiya ta tattauna da wadansu daga cikinsu inda suka bayyana irin mawuyacin halin da suka tsinci kansu a ciki da dalilin da suka sanya su tafiya kasar  Libiya a yunkurinsu na samun ingantacciyar rayuwa.

Malam Muhammad Sani Dahiru, magidanci ne da ya tafi kasar Libiya tare da matarsa da ’ya’yansa biyar, ya shaida wa Aminiya cewa shi mutumin Jihar Borno ne, kuma rashin zaman lafiya a yankinsu ne ya sanya shi barin kasar nan ya tafi Libiya, “Talauci da rashin tsaro ne suka fitar da ni daga gida zuwa Libiya, domin a hanya muka hadu da iyalaina gaba dayansu, wani lokaci an kai hari yankinmu haka muka fito babu komai tare da mu daga mu sai kayan jikinmu. Ganin irin tashin hankalin da muka shiga ne na yanke shawarar in tafi Libiya tare da iyalaina gaba daya, domin a wancan lokaci a gabanmu ake ta kashe mutane. Abin ba kyan gani ba dadin fada ko ina jini,” inji shi.                                                                                                                                                    Ya ce, “A wannan yanayi muka yi gudun hijira sai dai abin da muka tarar a Libiya ya fi abin da muka baro a gida muni, domin mun kasance ba ma aikin komai a kasar kullum muna waje guda a boye cikin fargaba da tashin hankali. Ana bin mutane ana farautarsu a koyaushe ana yi musu sata a kwace musu wayoyi, ko a sace su a mayar da su bayi. Shekaranjiya ma a gabana aka harbi wani abokinmu a kafa aka yi masa mummunan rauni kan wayar salularsa da suka nemi ya ba su ya ki. Aikin matasan kasar ke nan matasan su yi muku kwace su sayar da kayan su sha kwaya da kudin.”

Ya ce a baya shi dan kasuwa ne da ke sayen shanu a kasuwannin kauye da kan iyakar Kamaru ya kai Maiduguri ko Legas ko Fatakwal ya sayar, karayar arziki ya same shi ne sakamakon rikicin Boko Haram.

“Shekara biyun da na shafe a kasar Libiya ban tsira da komai ba, haka muka dawo daga mu sai jakar hannun. Ka ga da sauran rina a kaba ke nan, domin mun dawo ba komai ba mu da matsuguni ga iyali ka ga muna bukatar taimakon gwamnati domin gudun kada mu shiga wani hali. Mun gode wa gwamnati da ta dawo da mu gida, yanzu haka akwai tarin ’yan kasar nan da ke can Libiya da suke bukatar dawowa,” inji shi.

Hajara Muhammad uwar marayu shida ta shaida wa Aminiya cewa, ta tafi kasar Libiya ce bayan mijinta ya rasu ya bar ta da marayu shida.

Ta ce ita ’yar Jihar Kano ce, a Unguwar Kofar Mata, “Mijina ya dade yana jinya, ya rasu mako guda bayan da aka kai harin bam a Masallacin Juma’a na Kano. Dama sana’ar dinki nake yi da kula da yara, bayan rasuwar mijina, muka shiga wani hali sana’ar ta gagara bashi ya yi yawa sai muka tafi Libiya domin neman aiki. amma bayan zuwanmu kasar sai muka tarar babu kwanciyar hankali domin akwai ’yan kasar Larabawa da ake kira Haramaini da ke yawo a mota mai bakin gilashi inda suke sace mutane. Da zarar sun ga mutum sai su sace shi su yi masa kwace, su suna ganinka ta bakin gilashi kai ba ka iya ganinsu, a haka muka yi ta rayuwa. Akwai wani mutumin unguwarmu, shi ke ba ni dinkin jallabiya tun ban iya dinka jallabiya ba, a haka na koya ina yi, na tafi da ’ya’yana Hassan da Hussaini su kuma suna fita aikin gini. Amma su ma an dawo da su gida, jirginsu ya sauka kusan mako uku da suka wuce. Yanzu ni da karamar ’yata muka dawo, fatarmu gwamnati ta dube mu ta agaza mana. Idan aka dauki nauyin karatun ’ya’yanmu aka ba mu jari zamu yi sana’ar da za mu duba marayunmu,” inji ta.

Haka zalika Malama Isimaha ta ce ta yi ta gode wa Allah da Ya sanya ba ta dade a kasar Libya ba, kuma alheri ne dawo da su gida.

“Ni mai gidana ne ba ya da lafiya ya dade a kwance, ganin yadda ya bar ni ina ta fama da ’ya’ya 11 wahalhalu suka yi mana yawa lokacin da na ga ana ta tafiya Libiya sai mu ma muka je aka tafi da mu, domin mu samu aiki. Ko da muka je can sai muka ga abin ba haka yake ba, aiki wanki ne da ’yan aikatau. Sai mutum ya yini yana aikin har karfe daya na dare dan abin da ka tara sai Larabawa su ki ba ka, su hana maka kudinka sai in ka yi sa’a za su ba ka dan kadan. Dama ban shekara a can ba, na yi murna da aka dawo da mu, fatarmu gwamnati ta dubi halin da muke ciki a taimaka mana,” inji ta.

A bangaren Chikere Sidtus Obigbo mai shekara 27 cewa ya yi, ya tafi kasar Libiya ce shekara 6 da suka shude. Ya ce, iyayensa talakawa ba su iya daukar nauyin karatunsa bayan da ya kammala makarantar sakandare sai ya tafi Libiya domin neman rufin asiri ya kula da kansa da iyayensa. “Sai dai ba kamar yadda na zata ba, mu ’yan Najeriya da ke kasar Libiya mun samu kanmu cikin mummunan yanayi domin sai da aka sace ni aka yi garkuwa da ni aka nemi in fanshi kaina da kudin Libya Dinari dubu 10 (kimanin Naira miliyan daya da doriya). Kuma saboda ba ni da wannan kudi sai aka tsare ni a matsayin bawa aka kai ni cikin sahara na yi aikin hakar gwal tsawon wata 8, cikin mummunan halin kangin bauta da azabtar wa. Babu isasshen abinci babu kwanciyar hankali. Wani abin takaicin shi ne yadda ’yan Najeriya ke sayar da ’yan uwansu ga Larabawan Libya inda suke yin kashe-mu-raba, idan an kama mutum aka tsare shi sai a nemi ’yan uwansa a Najeriya su turo kudi su fanshe shi. Idan babu kudin sai a sayar da shi a matsayin bawa. Yanzu haka akwai wadanda ake tsare da su sama da shekara guda, sannan akwai matan da ake bautar da su a sanya su karuwanci da karfin tsiya idan sun ki a kashe su. Irin wadannan mata mafi yawansu ’yan makaranta ne da ake yaudararsu da sunan za a samar musu aiki a Turai. Akwai ’yan Najeriya da ke zuwa su dibi ’yan mata suna yi musu karyar cewa, suna da rumfunan kasuwaci ko wata masana’anta a Turai a haka suke yaudararsu su tilasta su karuwanci,” inji shi.

Ya ce, ya koyi sana’ar gyaran firiji da na’urar sanyaya daki kuma kafin ya tafi Libya, yana kasuwancin ne a Jihar Abiya inda yake sayar da man goge baki da buroshi.

“Ni dan asalin Jihar Imo ne, na gode wa gwamnatin kasata da ta dawo da ni gida, ina kira ga Gwamnan jiharmu ya ba ni jari domin in fara kasuwanci in taimaki rayuwata,” inji shi.

Bayanai sun nuna cewa mahukuntar kasar nan na ci gaba da daukar bayanan ragowar ’yan Najeriya da ke kasar Libya domin komo da su gida.