Aminiya

Muna bayan Siasia – Koci-Kocin Najeriya

Tsohon Kocin Super Eagles Samson Siasia

Kungiyar masu horar da wasan kwallon kafa ta Najeriya ta ce babu wani abin damuwa game da dakatarwar da Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya(FIFA) ta yi wa daya daga cikinsu Samson Siasia kan da zargin da ake yi masa na karbar rashawa da kuma sayar da wasa.

Ranar Juma’ar da ta gabata ce Hukumar FIFA ta fitar da sanarwa cewa ta dakatar da Siasia daga aikin horar da ’yan wasa har karshen rayuwarsa. Hukuma ta ce ta samu Siasia wanda tsoho Kocin Super Eagles ne da laifin cin hanci da rashawa. “Amincewar da ya yi cewa zai karbi cin hanci don sayar da wasa ya saba wa dokokin Hukumar FIFA,” inji sanarwar.

ADVERTISEMENT

Da yake tsokaci kan zargin da ake yi masa tsohon kocin wanda a baya ya horar da kungiyoyin kwallon kafa na Najeriya ’yan kasa da shekara 20 da ’yan kasa da shekara 23, ya yi fatali da wannan hukunci inda ya yi alkawarin wanke sunansa.

Shi ma da yake magana da Jaridar Aminiya Shugaban Kungiyar Masu Horar da Wasan Kwallo ta Najeriya, Koci Isah Ladan Bosso ya ce dukkan masu horar da wasan kallon kafa na Najeriya suna bayan Samson Siasia don tabbatar da an yi masa adalci.

ADVERTISEMENT

Ya ci gaba da cewa babu wani abu na damuwa ga ’yan Najeriya domin a shirye Siasia yake ya wanke kansa bisa wannan zargi da Hukumar FIFA take yi masa. Bosso ya kara da cewa kungiyarsu tana bin wannan batu cikin taka-tsantsan kuma ba za ta yi saurin yanke hukunci a kan zargin ba.

“Mu masu horar da wasan kwallon kafa muna da yakinin Siasia zai wanke kansa kan wannan zargi, don haka babu wani abu na damuwa a ciki. Ni kaina na taba fadawa cikin irin wannan hali, wanda ya faru musabbabin rashin fahimtar wani harshe. Amma da aka ba ni dama na wanke kaina, inda dakatarwar da aka yi mini ta shekara hudu ta koma ta wata hudu.

Don haka muna da yakinin shi ma Siasia zai wanke kansa daga wannan zargi kuma za a dage wannan dakatarwa da aka yi masa.don haka muna shawartarsa ya natsu sannan ya aiwatar da abin da ya kamata don ya wanke sunansa,” inji Bosso.