✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muna bukatar zabe ba tare da kula da addini ko kabila ba – Sarkin Musulmi

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya ce al’ummar kasar nan na bukatar zabe sahihi kuma ingantacce a shekarar 2015 wanda bai dauke da…

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya ce al’ummar kasar nan na bukatar zabe sahihi kuma ingantacce a shekarar 2015 wanda bai dauke da nuna bambancin addini ko kabila.
Sarkin Musulmi ya yi bayyana haka ne a fadarsa a ranar Litinin da ta gabata lokacin da yake karbar Jakadan Amurka a Najeriya Mista James Entwistle da ya kai masa ziyara ban girma.
Ya yi kira a dauki matakin magance ta’addanci da lalaci a kasar nan domin suna yin tarnaki ga ci gaban kasa.
Alhaji Sa’ad ya kara da cewa ta’addanci da hatsaniya da tada zaune-tsaye sun saba wa koyarwar manyan addinanmu biyu, kuma ga shi suna kokarin zame wa kasar nan kadangaren bakin tulu. “Ba wani mutum da ke son kasar nan ta tsundumma cikin hatsaniya da fadace-fadace da matsalar kunar bakin wake da sauran abubuwan lalaci da suka shigo mu,” inji Sarkin Musulmi.
Sarkin Musulmi ya ce “Mutanen kasar nan na bukatar kwanciyar hankali da lumana, a koyaushe suna bukatar ’yanci a matsayinsu na ’yan kasa.”
Ya nuna gamsuwarsa da yadda Najeriya da Amurka suke hulda a fannin lafiya da kwanciyar hankali da ilimi da siyasa da sauransu.
Tun farko Jakadan ya nuna gamsuwarsa kan gudunmawar da Sarkin Musulmi ke bayarwa ga dorewar zaman lafiya a Najeriya da wasu bangarorin duniya. Ya ce da’irar da aka yi ta fahimtar addinai a kasar nan abu ne mai kyau da Sarki ya aiwatar kuma shi ne zai hana rarrabuwar kawaunan jama’a.
Ya ce yana fata ’yan Najeriya za su kauce wa abin kunya a zaben 2015, su tsaya kai da fata su yi zabe na gaskiya wanda yake sahihi kuma ingantacce.