✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muna duba hanyoyin sallamar ’yan N-Power – Ministar Ayyukan Jinkai

A kwanankin baya ne Ministar Ayyukan Jinkai da Magance Annoba da Jin Dadin Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouk, ta ziyarci hedkwatarmu a Abuja, inda ta…

A kwanankin baya ne Ministar Ayyukan Jinkai da Magance Annoba da Jin Dadin Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouk, ta ziyarci hedkwatarmu a Abuja, inda ta amsa tambayoyin Aminiya game da shirin gwamnati na yin adabo da matasa masu cin gajiyar tallafin N-Power da kuma nasarorin da aka samu a shirin ciyar yaran makaranta da tsarin da gwamnati ke yi na sake tsugunar da ’yan gudun hijirar cikin gida:

Bisa dukkan alamu, ayyuka sun sha kan ma’aikatarku; kama daga tallafa wa ’yan gudun hijirar cikin gida da magance bala’o’i da ma shirye-shiryen Gwamnatin Tarayya na tallafi ga masu karamin karfi. Yaya ki ke gudanar da wadannan tarin ayyuka?

Eh, zancen gaskiya kamar dai gagarumin aiki ne; sai dai suna da alaka da juna. Gwamnati cikin hikimarta ta ga dacewar a samar da ma’aikatar da za ta rika kula da wadannan batutuwa. Muna samun aukuwar bala’o’i nan da can, wanda hakan ya haifar da bukatar ayyukan jinkai da  na zamantakewa. Don haka, ma’aikatar daya ce, sakamakon batutuwa masu kama da juna ne; kuma mun dukufa ka’in-da-na’in wajen ganin ba mu bai wa ’yan Najeriya kunya ba.

Masu cin gajiyar tallafin N-Power suna cikin zullumi da fargaba saboda yadda ake yamadidi cewa akwai yiwuwar gwamnati ta sallame su. Kwanaki wata jarida ta wallafa cewa ’yan N-Power dubu 200 gwamnati ba za ta biya su alawus na watan Janairu ba, ko za ki yi tsokaci kan haka?

Ban ga dalilin da cikinsu zai duri ruwa ba. Shirin na N-Power dai wani tsari ne na gwamnati domin dafa wa matasanmu marasa abin yi. Mun faro kashin farko na shirin a 2016 da ya kamata a ce tun 2018 an sallame su, amma sakamakon rashin kyakkyawan tsari a kasa sai aka kara musu wa’adin. Don haka, sun kwana da sanin cewa tun farkon shirin dama shekara biyu ne kacal za su yi suna amfana; ba na dindindin ba ne.

Gwamnati tana son ta dafa musu wajen samun abin zaman gari, kuma mun yi imani cewa galibin masu hankali cikinsu sun dan yi tattali daga abin da muke biyansu a wata. Har wa yau, sun samu horo kan wasu sana’o’in da za su zama masu dogaro da kai. Don haka ina ganin babu dalilin zama cikin zullumi. Tun farkon al’amarin ai sun kwana da sanin cewa shirin na wani takaitaccen lokaci ne.

A nan ma’aikatarmu, muna nazarin hanyoyin da za a bi wajen adabo da su. Ba kawai za mu sallame su ba ne mu bar su hakan nan, muna da tanadi, kuma muna kan bijiro da tanade-tanaden. Muna da tsarin sallamarsu cikin makoma mai kyau domin su samu tudun dafawa bayan sallamar.

To yaushe ne za a sallame su?

Yanzu ne fa shekarar ta fara; muna dai tunanin kafin karewar shekarar, muna tunanin bullo da dabarun sallamar tasu.

Batun ’yan gudun hijirar cikin gida, na daga cikin matsalolin da kasar nan ke fuskanta. Ko ma’aikatarku tana da alkaluman ’yan gudun hijirar? Na biyu kuma akwai kungiyoyin agaji masu yawa da ke bugun kirjin gudanar da ayyuka makamantan naku, kamar me kuke yi takamaimai don kawo karshen matsalar?

Ina ganin dalilin kirkiro da wannan ma’aikatar shi ne don hada hancin dukkan wadannan kungiyoyi da ma ayyukan agajin karkashin inuwa guda da zimmar samar da sakamako mai kyau. Ma’aikatarmu tana kan shirin yadda za ta kyautata tsarin kuma za mu bullo da dabarun yadda za mu aiwatar da tsarin.

Akwai korafe-korafe cewa ana karkatar da akalar tallafin da ake kai wa ’yan gudun hijira. Me ma’aikatarki ke yi kan haka?

Muna yin duk mai yiwuwa don dakatar da hakan. Muna da hukumomi a ma’aikatar wadanda hakki ya rataya a wuyansu wajen mika wa ’yan gudun hijirar kayayyakin tallafin. Mun tsawatar wa masu aikata haka. Kuma ina da yakinin sun dauki darasi. Ba na tunanin akwai wanda zai sake azarbabin aikata ba daidai ba. Da zarar mun samu aikata haka, to mukan yi gaggawar daukar matakin da ya dace.

Kwanaki mun yi wani labari game da yadda sansanonin ’yan gudun hijira ke neman zama gidaje na dindindin. Me ma’aikatarki ke yi don su koma gidajensu?      

A farko na ce, ma’aikatata ta mayar da hankali kan sake musu matsugunai tare da mayar da su muhallansu, amma akwai bukatar taka tsantsan. Za mu mayar da su garuruwansu ne kawai idan wuraren sun zama babu barazanar tsaro. Muna tattaunawa da Gwamnan Jihar Borno, wanda shi ma ya damu sosai wajen ganin sun koma garuruwansu kuma mun riga mun fara shirin sake gina musu muhallansu.

Shugaban Kasa, ya sahale a fitar da kudaden aiwatar da wannan aiki ta hannun Hukumar Kula da Ci Gaban Arewa maso Gabas. Za mu duba wuraren da akwai tsaro cikinsu. Ba abu ne na kwana guda ba; amma dai mun dukufa wajen ganin mun mayar da su garuruwansu idan yanayin tsaro ya inganta.

Kina ganin shirin dafa wa yaran firamare abinci zai dore; kuma yaya za a shigar da jihohin da har yanzu ba sa cikin tsarin?

Yana samun nasara sosai kuma ya dore. Gwamnatin Tarayya tana gudanar da tsarin ne tun shekarar 2016. Mun faro ne da jihohi kadan, amma yanzu kusan dukkan jihohin  kasar suna ciki, har ma da Birnin Tarayya, Abuja. Muna kira ne kawai ga jihohin da su shiga sahu tare da ci gaba daga inda Gwamnatin Tarayya ta tsaya. Abin da muka sani a nan shi ne Gwamnatin Tarayya tana samar da abinci sau daya a rana ga daliban firamare aji daya zuwa na uku. Muna fata gwamnatocin jihohin su dauko daga aji hudu zuwa shida. Kuma na yi amanna cewa sun ga alfanun shirin; don haka za su iya ci gaba daga inda muka tsaya.

A kasafin bana, an rage kudin da aka ware wa ma’aikatarki. Ko akwai yiwuwar ma’aikatar ta lalubo tallafi daga wasu kafofi na daban?

Ina da tabbacin gwamnati ta yi haka ne sakamakon lura da abin da ke a lalitarta. Mu a nan, muna duba hanyoyin hada gwiwa da masu ruwa-da-tsaki a harkar domin samun tallafi tare da dafa wa gwamnati. Gwamnati kawai ba za ta iya abin ba. Muna tsammanin tallafi daga attajiran kasar nan da masu halin taimako da kungiyoyi domin su shigo ciki wajen magance matsalolin jinkai a Najeriya.

Yaya rayuwarki take koma-bayan aikin gwamnati?

Mutane suna cewa wai ai ni bana son mu’amala da mutane, eh na yarda. Ban cika son hayaniya ba. Ina son zama a gida ni kadai. Amma kuma ina duba hanyoyin da zan taimaka wa mutane; saboda ina jin ba zan samu natsuwa bai idan ban taimaka wa mutane masu bukatar taimako ba. Gani nake kamar Allah Yana kallona. Ni mutum ce mai son zama da iyali kuma ina jin dadin zama cikinsu, har da abokai.

Amma yawanci in mutum ya zama minista ya kan canja abokai. Ban san ko ke kin canja abokai ba?                                                                                      

Ni ba mutum ba ce ta daban ba. Ni mai ba mai inda-inda ba ce. Eh, lallai ne ba za ka saurari kowa da kowa ba; amma ai ka san su wane ne abokanka na kwarai. Ina son mutane masu gaskiya wato kaifi guda.

Wane irin abinci kika fi so?

Kasancewa ta Bafulatana ’yar asali, gaskiya ina son tuwo da miyar kuka. Ina kuma son fura da nono. Duk da yake ba na cin tuwo da daddare, na fi cin tuwo a matsayin abincin rana. Ina kuma son sakwara; a takaice ina son duk wani abinci mai nauyi.

A kwanakin baya sunanki ya shiga kanun labarai game da batun labarin karya cewa za ki auri Shugaba Buhari. Ko za ki bayyana mana yadda kika jure wannan lamari?

Eh, kamar yadda ka ce ai labarin na karya ne; kuma na gaya maka cewa ni ba na boye-boye a al’amurana. Kamar yadda abin ya zo, haka nan ya wuce. Kuma tun farkon abin ma ai na ce zai zo ya kuma wuce; kuma jama’a za su san gaskiyar lamarin daga karshe. Don haka ya faru ya kare ai.

Kuma ko kin hadu da matar Shugaban Kasar tun daga lokacin?

Eh, a gaskiya ba mu hadu ba har yanzu. Saboda ayyukanmu sun bambanta; sha’aninta daban da nawa. Kamar yadda kuka sani watakila ayyuka sun sha mata kai, ni ma haka nan. Amma babu wata jikakka a tsakininmu.

To batun karatu ko kina karanta kagaggun labarai? Kuma ko kina kallon fina-finai irin nasu Kannywood da Nollywood, kuma wane kika fi so?

A baya can ina taba karatun littafai; amma yanzu ina ganin watakila saboda aikin da nake yi da sauran ababuwan rayuwa na daina gaskiya. Ina da ababuwa da dama da ya kamata in karanta da suka shafi aikina. Akwai yiwuwar in koma karatu nan gaba, amma yanzu kam, sai a hankali. Nakan kalli fina-finai musamman idan ina zaune cikin masu kallo. Dukkansu ina sonsu da Kannywood da Nollywood din, suna kokari, gaskiya.