✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muna fama da karancin ma’aikata –Daraktan Doas

Daraktan Hukumar Kula da Tallace-Tallace Allunan kan Hanya da Wuraran Kasuwanci (DOAS) ta Birnin Tarayya Abuja Alhaji Babagana Ahmad, ya ce hukumarsu tana fama da…

Daraktan Hukumar Kula da Tallace-Tallace Allunan kan Hanya da Wuraran Kasuwanci (DOAS) ta Birnin Tarayya Abuja Alhaji Babagana Ahmad, ya ce hukumarsu tana fama da karancin ma’aikata.  Alhaji Babagana Ahmad ya bayyana haka ne a shekaranjiya Laraba yayin ziyarar da ya kawo hedkwatar Kamfanin Media Trust mai buga jaridun Daily Trust da Aminiya da ke Abuja. Ya ce  hukumarsu tana matukar kokari wajen sama wa Hukumar Birnin Tarayya Kudaden shiga da sauran kananan hukumomi da suke karkashinta.

Daraktan ya ce “Hukumarmu tana fama da rashin issasun kudade da za ta rika gudanar da aikinta da karancin ma’aikata da karancin kayan aiki da rashin motocin zirga-zirga da kuma rashin wadataccen filin da za mu fadada ofishinmu.”

Ya ce ayyukan hukumar sun kunshi kula da tabbatar da cewa dukkan wuraren da ake gudanar da kasuwanci a Abuja suna biyan kudaden da hukuma ta sanya. Kadan daga cikin wuraren kasuwancin da hukumar take da alhakin ganin sun biya haraji sun hada da manyan shaguna  (plaza) da gidagen mai da asibitoci da bankuna da makarantu da otal-otal da dukka wajen da ake gudanar da kasuwanci a Birnin Tarayya.

Daraktan ya ce “Daga farkon bana zuwa watan Agusta hukumar ta samar da sama da Naira miliyan 300 yayin da muke sa ran za mu ninka a badi.”

Da yake bayani a kan cin gashin kai da hukumar take nema daga bangaren hukumar birnin na tarayya ya ce “ Ya kamata a ba mu cin gashin kai kamar yadda Hukumar FCT-IRS da sauran hukummomin haraji suke cin gashin kansu idan gwamnati ta yi haka za ta kara bunkasa hanyoyin tara haraji na hukumar.”

Daga karshe Daraktan ya nemi Kamfanin Media Trust ya hada kai da hukumarsa wajen wayar wa jama’a kai a kan biyan haraji da kuma fahimtar da su aikin hukumar.