Muna goyon bayan kudurin hana bara a Kano – Kabiru Alasan

Shugaban kwamitin aiyuka da sufuri da gidaje na majalisar wakilan jihar Kano, Honarabil Kabiru Alasan ya ce, majalisar jihar za ta goyi bayan kudurin dokar hana barace-barace don ci gaban jihar.
Honarabil Kabiru Alasan dan asalin unguwar Katanga da ke garin Rurum, wanda ke wakiltar karamar hukumar Rano ta jihar Kano ya yi bayanin ne a tattaunawarsa da Aminiya a jihar.
“ ‘Kamar yadda ka sani na farko dai har yanzu hukumar Hisba ba su kawo mana kudirin ba. Kuma mu da muka fito daga jihar Kano musulmi ne masu aiki da musulunci, kuma addininmu ya yi hani da bara, ba tare da wani dalili ba. Kuma an hana zaman banza da tumasanci. Barace-barace a kan tituna na da illa sosai. Wannan kudiri da hukumar Hisba za ta kawo majalisa ya na da muhimmaci. Saboda haka za mu yi iya kokarin mu wajen ganin mun duba kudirin, kuma mun duba abubuwan da ke cikin sa. Duk abubuwan da muka san ba zai cutar da al’ummarmu ba, za mu goyi bayan sa,” inji shi.
Ya kara da cewa kalubalen da yake ci masa tuwo a kwarya shi ne rashin fahimtar aiki dan majalisa da wasu jama’a ba su yi ba.
‘Duk wani dan majalisa yana fuskantar wannan matsala. Sau da yawa mutane za su zo wurin dan majalisa su rika tambayarsa kudi ko kuma su dora masa wani nauyi  da ba shi da iko a kai. Shi dan majalisa aikinsa shi ne ya yi dokar da za ta amfani jama’a’. In ji shi
Alhaji Kabiru wanda tsohon sakataren kasuwar Mil 12 ne ya yi watsi da zarge-zargen da wasu ke yi cewa ’yan majalisar sun zaman ’yan amshin-shatan bangaren zartarwar jihar.
Ya yaba wa ’yan majalisar kan hadin kai da goyon baya da suke ba wa shugabancin majalisar.
‘Tun da muka zabi sabon shugaban majalisarmu Rait Honabil Gambo kiru aka sami zaman lafiya da kwanciyar hankali a majalisar, domin duk da ya kada ni yi a zaben shugaban majalisa ba na yi masa hassada, tun da damokradiyya aka yi. Ina yi masa fatan alheri da daukacin sauran ’yan majalisar’. In ji shi.