Search
Subscribe
Muna kokarinmu wajen samar da tsaro- Buratai

Muna kokarinmu wajen samar da tsaro- Buratai

Babban hafsin sojojin Najeriya, Tukur Yusuf Buratai ya yi magana game da kashe-kashen da ke faruwa a jihar Zamfara.

Bayan da aka tambaye shi wasu na ganin sojojin sun gaza bisa la’akari da cewa ana garkuwa da mutane duk da cewa sun ce suna kokari.

Sai ya ce “duk wanda ya ce sojoji ba sa kokari bai san sha’anin tsaro ba.”

Ya kara da cewa shi tsaro ana fara shi ne daga matakin fako – wato daga kan jama’a.

Ya bayyana cewa sojoji na iya bakin kokarinsu domin tabbatar da cewa suna kare rayukan jama’ar kasar.

An kashe akalla mutum 3,500 yayin da wasu 9,000 suka jikkata a tsawon shekara biyar, kamar yadda sakataren gwamnatin jihar Farfesa Abdullahi Muhammad shinkafi ya shaida wa BBC.

Ya ce alkalunma sun nuna cewa kimanin kauyuka 500 ne aka kai wa farmaki, yayin da aka lalata kuma aka bata hekta 13,000 na kasar gona.

Farfesan ya ce sun tantance hakan ne saboda duk lokacin da ‘yan bindiga suka kai hari gwamnatinsu tana tura tawaga a kai taimako ga iyalan mamata da wadanda suka jikkata da kuma wadanda suka rasa dukiya.

Har ila yau ya ce akwai mutane da dama da rikicin ya raba da muhallansu. Ya kuma ce rikicin ya fi shafar harkar noma.

Ya ce suna ba jami’an tsaro dukkannin goyon bayan da ya dace wajen ganin an kawo karshen kashe-kashen da ke faruwa a jihar.

A karshen makon jiya ne gwamnatin tarayya ta dakatar da aikace-aikacen hakar ma’adanai a jihar.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin