✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muna maraba da shigowar Kwankwaso Jam’iyyar APC – Gaya da Kawu Sumaila

A yayin da wasu ke bayyana tsoro da damuwa kan yiwuwar Gwamnan Jihar Kano Injiniya Rabi’u Kwankwaso da Gwamnonin G-7 na PDP su koma sabuwar…

A yayin da wasu ke bayyana tsoro da damuwa kan yiwuwar Gwamnan Jihar Kano Injiniya Rabi’u Kwankwaso da Gwamnonin G-7 na PDP su koma sabuwar Jam’iyyar APC, Sanata Kabiru Ibrahim Gaya na mazabar Kano ta Kudu cewa ya yi “Muna marhabin da shigowar Kwankwaso cikin jam’iyyarmu.”

Sanata Gaya wanda ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da ’yan jarida a Kano, inda ya ce ba ya wani dar-dar game da shigowar ta Kwankwaso cikin jam’iyyar ta APC, “domin babu wani mutum da zai hana ka samun rabonka, don haka shigowar Kwankwaso za ta kara karfi ga jam’iyyar ta kara karbuwa ga jama’a a jihar,” inji shi.
Ya ce babu wani dan jam’iyya mai kishinta da ba zai yi farin ciki ba, idan ya ga tana samun karbuwa a wurin jama’a. Ya ce idan Kwankwaso ya shiga APC ba abin da zai faru, illa a zauna da shi a tattauna makoma da yarjejeniya a kan tafiyar da jam’iyyar.
Sanata Gaya ya ce abin da ya sa ba a gan shi tare da tawagar jiga-jigan APC lokacin kai wa Gwamna Kwankwaso ziyara ba, shi ne wannan magana ce da ta shafi shugabancin jam’iyya, kafin daga bisani kowa ya tsoma baki a ciki.
Shi ma dan Majalisar Tarayya Sulaiman Abdurrahman Kawu Sumaila mai wakiltar Takai da Sumaila ya ce shigar Gwamna Kwankwaso cikin jam’iyyarsu ta APC ba za ta girgiza su ba.
dan majalisar wanda ke da burin tsaya wa jam’iyyar takarar Gwamna a zaben 2015 ya bayyana haka ne a hira da gidan Rediyon Freedom a Kano.
Kawu Sumaila ya ce shigar Gwamna Kwankwaso cikin Jam’iyyar APC ba zai sa shi ya fita daga cikinta ba, sai dai idan an yi masa rashin adalci. “Babu wanda ya san gobe sai Allah, ba zan fita daga Jam’iyyar APC ba saboda shigar Gwamna Kwankwaso. Zan tsaya in karbi ’yancina da na wadanda muke tare, saboda wahalar da muka sha wajen kafa wannan jam’iyya, domin sai da
muka dauki tsawon wata shida muna shige da fice kafin tabbatuwarta. In takaice maka duk wanda ya ji sunan Jam’iyyar APC a Kano, to daga bakina ya fara jin ta. Amma idan kaddara ta zo aka yi wa Kawu rashin adalci, wannan wani abu ne na daban. Irin haka ta faru a Shekarar 2003 da na ga an yi min rashin adalci sai na fita daga Jami’yyar PDP.”
dan majalisar ya kara da cewa Jam’iyyar APC na maraba da shigowar Gwamnoni G7 cikinta, sai dai inji shi ba za su yarda a yi komai a lullube ba don haka za su ba kowa dama ya je ya yi rajista da jam’iyyar a mazabarsa.