✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muna maraba da shirin gwamnati na farfado da noman auduga – Ma’aji

Alhaji Abubakar Sadik Sanyinna shi ne Ma’ajin Kungiyar Masu Aiki da Auduga ta Kasa, manomin auduga a Sakkwato da Zamfara a tattaunawa da Aminiya, a…

Alhaji Abubakar Sadik Sanyinna shi ne Ma’ajin Kungiyar Masu Aiki da Auduga ta Kasa, manomin auduga a Sakkwato da Zamfara a tattaunawa da Aminiya, a wata gonarsa, a Karamar Hukumar Wamakko a Jihar Sakkwato  a makon jiya, ya ce shirin Gwamnatin Tarayya na bayar da tallafi ga manoman auduga, zai farfado da noman auduga a Najeriya:

 

Me za ka ce  kan shirin Gwamnatin Tarayya ta hannun Babban Bankin Najeriya (CBN), na bullo da shirin tallafa wa manoman auduga a kasar nan?

Kamar yadda aka sani noman damina na karatowa, a watan biyar (ko shida) ake samun ruwan sama. A bana  Gwamnatin Tarayya a karkashin kular Babban Bankin Najeriya (CBN) ta hanyar kungiyar masu aiki da auduga ta kasa ta shigo ciki za ta ba da tallafi ga manoman auduga, domin ta ga alfanun abin a kan manoman shinkafa da aka bai wa tallafin gwamanti ta hannun Bankin CBN. Abin ya bunkasa noman shinkafa, ita ma auduga na da wannan bukatar  da zarar an soma wannan shirin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar a watan nan na Mayu, kuma gudunmuwar ta shiga hannun manoman auduga, to shirin zai samu nasara don za a habaka noman auduga a Najeriya.

An dade ana noman auduga a Najeriya, amma nomansa ya kasa bunkasa, wane alfanu yake da shi ga ’yan Najeriya da har sai Gwamnatin Tarayya ta yi masa shiri na musamman?

Kamar yadda ka ce noman auduga tsohon lamari ne ana yin sa, tun lokacin da ba a iya gurza  audugar da inji. Mahaifanmu shekara 50 da suka wuce, sukan gurza auduga, su fitar da irinta daban, ita daban su markade ta, a yi sabi ta hanyar gargajiya daga baya aka samu na’urar zamani. A baya-bayan nan ne kamar shekara biyar da suka wuce, aka samu tabarbarewar noman, inda ya yi kasa, saboda matsalolin rashin samun iri ingantacce. Bayan farashinta ya yi kasa uwa uba ga rashin tallafi daga gwamnati, amma yanzu ta gano muhimmancin noman auduga da rawar da take takawa a kasa, in aka yi la’akari da tun daga manomanta zuwa masu sarrafa ta da kai ta masaku, magurzar auduga daya na iya daukar mutum 500 aiki. In aka samar da magurza 20 a kasa ka lissafa ka gani can baya akwai masaku da yawa, amma da noman ya ja baya duk sun mutu. Uku kawai ke aiki a yanzu. Da alama gwamnati ta sauya tunaninta ne, ta yi nazarin noman auduga na cikin lamarin da ke samar da abin yi ga matasa kuma hakan zai taimaki gwamnati a wannan bangare, don ba ta iya bai wa kowa aiki. Samar da irin audugar, ya nuna gwamnati ta fito sosai da nufin farfado da noman auduga.

To kamar da wane lokaci ne auduga take yi?

Auduga ba kamar sauran abubuwa ba ne, da ba su yi in akwai karancin ruwan sama; irin su gero da ba ya yi sai da ruwan sama. Ana noman auduga da rani ta yi kyau, kamar yadda ka gani a gonata ta yi kyau kamar a cikin damina. Kowane lokaci tana yi, ba sai da ruwan sama ba. Sai dai nomanta a rani ya fi na damina wuya a bangaren ban-ruwa da kulawa. Amma irin su daya ne da na damina da rani. Babu bambanci kowane ka sanya zai yi, don ni irin damina ne na shuka yanzu a rani.

Wane kira kake da shi ga gwamnati a kan ta kara tsaya wa noman auduga?

Kirana ga gwamnati  ta kara tsaya wa manoman auduga,  hakan zai sanya a samu audugar ta yi yawa har a rika kai ta kasashen waje, kamar a baya can. Ko ba komai audugar Najeriya tana da kyau in akwai ta a kasuwa ba a barin ta a dauki wata. Sannan duk abin da ake nomawa ba wanda ya yi darajar auduga, don ita kadai ce manominta ba ya zuwa talla har gida ake samunsa a saya, ba wani bata lokaci mai saye ba ya damuwa da nisan wuri. Kuma ko shekara nawa aka ajiye ta ba ta lalacewa  ya kamata a karfafe su, su rika noma abin da aka gada kaka da kakanni. Bayan man fetur, ba abin da ya kai auduga kawo kudi.

A nan Sakkwato, ba mu da magurza. In mun noma muna kiran mutane daga Kebbi ko Zamfara su zo su saya. A farkon kakar auduga na sayar da tan daya Naira dubu 200, amma yanzu ta rage kudi, tan daya ana sayar da shi Naira dubu 150 zuwa dubu 160. Gonata ta Sakkwato, wadda na shuka auduga kadada (hekta) daya ce in na samu iri mai kyau na kula da ita sosai, na sanya mata taki kamar buhu shida zan samu tan biyu har zuwa biyu da rabi na audugar. Ka ko ga a haka dai gwargwado an samu. Abin da ya sanya muka kara jin dadi ga wannan shirin da Shugaban Kasa zai kaddamar a Jihar Katsina, kan farfado da noman auduga a Najeriya, ba wani manomi da ba zai yi maraba da shirin ba, don taimakon kasa ce.