✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muna rayuwa cikin kunci maimakon samun ilimi – Almajiran Daura

Makarantar Allo ta Malam Bello Abdullahi da ke cikin garin Daura na daga cikin makarantun da ke kula da kangararrun yara sama da shekara 40.…

Makarantar Allo ta Malam Bello Abdullahi da ke cikin garin Daura na daga cikin makarantun da ke kula da kangararrun yara sama da shekara 40.

Malam Bello ya shahara wajen tarbiyyar kangararrun yara wanda hakan ya sa ake kawo masa yara daga kasashen irin su Jamhuriyyar Nijar da Benin da sauransu. A ranar Lahadin da ta gabata wadansu daga cikin daliban makaranta sun yi zanga-zangar da ta jawo hankalin jama’a da ’yan sanda.

Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Katsina, Sanusi Buba ya ce rahoto ne ya zo musu cewa almajiran makarantar sun yi bore saboda kuncin rayuwa da luwadi da suke zargin ana yi da wadansu daga cikinsu, inda suke koka kan malamansu musamman dan Malam Bellon mai suna Umaru da Sarkin Gida Malam Sa’adu mai lakanin Dankani sai kuma Malam Hassan.

A lokacin da aka ziyarci gidan, Aminiya ta yi karo da tarin alluna a wajen gidan, sai dai kuma babu wata alama ta inda aka ajiye Kur’anai da ke nuna ana amfani da su. Akwai kananan dakuna shida a gidan wadanda suke kamar na gidan yari domin dukkansu an yi musu kofar rodi. Kuma babu tsabta a gidan.  “Mu 300 ne ke zaune. Kowane daki ana sanya mutun 40 ko fiye da haka in lokacin barci ya yi. Sai a daure mana hannuwa ta baya da kafafu. Sannan kullum sai an yi mana bulala 30. Goma da safe in za a ba mu tuwon safe, haka na rana da na dare. Sai mu yi mako ba mu yi wanka ba domin babu ruwan,” inji wani daga cikin kangararrun daliban.

Wani yaro mai kimanin shekara 13 mai suna Ali ya ce shekararsa uku a gidan, kuma iyayensa ne suka kawo shi saboda sace-sacen da yake yi. Amma tunda aka kawo shi ba a taba ba shi magani ya sha don ya bar halinsa ba. Matasan sun tabbatar da cewa iyayensu ne suka kawo su, kuma an kawo su ne da nufin su gyaru a kan mugayen halayen da suka shiga da samun ilimin addini.

Fahad Jibrin ya ce an kawo shi ne daga Mubi a Jihar Adamawa saboda shaye-shayen da ya fara, kuma ya ce shekararsa 5 a gidan, amma in baya ga azaba babu abin da ake yi masa. Sannan ya nuna wadansu mutun biyu da ya ce da hankalinsu aka kawo su, amma yanzu duk sun haukace. Sannan ya ce yana cikin gidan mutum  shida suka rasu.

Shi kuwa Zahra ya bayyana yadda su Malam Umaru suka yi amfani da karfinsu suka yi luwadi da shi. Ya ce babu yadda zai yi da su domin su ne ke tafiyar da gidan sai yadda suka ga dama suke yi kuma a gaban idon kowa. Almajiran sun ce duk wani abin da za a kawo musu daga wajen iyayensu, sai dai su ji labarin an kawo, amma ba a ba su. Kuma in an zo ganinsu, ba a bari a shiga gidan sai dai a ce musu su ce ana kula da su sosai, kuma ana ba su duk wani abin da aka kawo.

Da Aminiya ta so jin ta bakin makwabtan makaranta, sun ki su yi magana, amma wani da ba ya so a ambaci sunana ya ce abin da ya sa ba su damuwa da duk wata hayaniyar da suke ji daga gidan shi ne saboda sun san wadanda ke ciki. Kuma kullum ana fito da su waje da yamma don yin karatu. Ba su zuwa ko’ina daga inda suke, kuma suna ba hanya baya don kada ma su rika ganin masu wucewa.

Da Kwamishinan ’Yan sandan ya je gidan Sarkin Daura, Dokta Farouk Umar Farouk, ya shaida masa halin da suka tarar  da makarantar.

Sarkin Daura ya nuna bacin ransa kan irin yadda aka samu faruwar wannan al’amari a garin Daura, inda ya ce, “Wannan Daura da Daurawa aka bata wa suna. Malam Bello ka ci amana. Kana daga cikin mutanen da nake ba hannu mu gaisa don girmamawa, amma ka zo kana aiwatar da wannan mummunan aiki haka.” Sannan Sarkin ya ce ’yan sanda su ci gaba da aikinsu.

Aminiya ta yi kokarin zantawa da wani daga cikin iyayen yara amma babu wanda ke cikin garin na Daura. Sai dai ta samu zantawa da wani wanda ya ce ya zauna cikin gida kusan sau 9, “Duk abin da ake fadi ana yi a gidan babu karya. Su wadannan da ke kula da gidan duk suke da wannan matsalar. Shi Malam sai ya yi wata biyar zuwa bakwai bai zo gidan ba. Amma gaskiyar magana babu gyara tarbiyyar da ake yi. Ka ga wadancan shagunan uku na rufe? Babu abin da ke cikin sai yaduka da shaddodi da kayan abinci iri-iri wadanda iyaye ke kawo wa ’ya’yansu amma ba a ba su. Gaskiya abubuwan sai dai a yi shiru kawai,” inji shi.

Malam Bello wanda shi ne mai makarantar ya musanta zargin da ake yi masa. Sannan ya ce a iya saninsa ana kula da yaran kuma ana ba su karatu tare da kula da tarbiyyarsu. Batun aikata wasu laifuffuka da aka ce ana yi ya ce ba zai ce komai ba, sai dai su wadanda yaran suka ambata ne za su iya magana.

A shekaranjiya Laraba ma ’yan sanda sun sake kai mamaya wata makarantar allo a garin Katsina bisa irin wannan zargi.