✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muna shirin samar wa manoman Arewa taki a Legas – Sa’du Gulma

Alhaji Sa’adu Gulma Shugaban Kamfanin Dabi ya shaida wa Aminiya shirin da gwamnatin Legas ke yi tare da hadin gwiwar kamfanin don ganin ta fara…

Alhaji Sa’adu Gulma Shugaban Kamfanin Dabi ya shaida wa Aminiya shirin da gwamnatin Legas ke yi tare da hadin gwiwar kamfanin don ganin ta fara samar da taki ga manoma a Arewa. Ya kuma yi tsokaci kan yadda cikin dan lokaci Shugaba Buhari ya yi nasarar janyo hankalin al’ummar kasar kan sana’ar noma:

Wane ne Sa’adu Gulma?

Sunana Alhaji Sa’adu Gulma Shugaban Kamfanin Dabi kuma Mataimakin Shugaban ’Yan Arewa mazauna Legas na Jam’iyyar APC. ni mutumin Jihar Kebbi ne, na kwashe sama da shekara 20 ina harkokin saye da sayarwa a kasuwar canjin kudaden kasashen waje, kafin daga bisani in sauya akala in shiga bangaren harkokin noma da sufuri da hada-hadar kasuwanci.

Mene ne dalilin da ya sa ka sauya akala daga sana’ar da ka shafe sama da shekara 20 a ciki?

Godiya ta tabbata ga Allah Mai komai Mai kowa, Shi ke yin yadda Ya so a lokacin da Ya so. Tabbas na shafe sama da shekara 20 kasuwar hada-hadar kudaden waje wacce aka fi sani da kasuwar canji. Yanzu kuma gani a cikin harkar noma da sufuri. Kamar yadda ka sani ne, akwai dama da yawa a kasarmu Najeriya. Kasarmu kasa ce da ke makare da dimbin arziki a kowace jiha a kuma kowane yanki. Dalilin da ya sa ake ganin kasar nan da talauci matsalar shugabanci ce, a baya an yi sake, shugabannin kasarmu sun gaza samar da hanyoyin da za a ci gajiyar dimbin arzikin kasa, an dogara kacokan a kan arzikin mai.

Jihohinmu da dama ba sa iya dogaro da kansu sai da abin suke samu daga Gwamnatin Tarayya bayan a kasar nan kowace jiha tana da arzikin da in ta tattala shi za ta rike kanta. Amma alhamdulilahi a yanzu an dauko hanyar gyara, sababbin sauye-sauyen da Shugaba Buhari ya zo da su a wannan karo sun fara sauya tunanin al’umma yanzu jama’a da dama sun fara sauya salo domin ganin sun amfana da arzikin da a baya aka yi watsi da shi.

A baya gwamnatin Jihar Legas ta ba ka aikin tsabtace wani sashi na Kasuwar Shanu ta Agege inda wajen zubar da shara ne ka mayar kasuwa a yau, ko yaya aka kai ga haka?

Tabbas a baya a Kasuwar Shanu ta Duniya da ke Legas akwai sashin da ke ci wa gwamnati jihar tuwo a kwarya, wuri ne da aka mayar wajen zubar da shara shekaru aru-aru, kuma yake barazana ga muhalli da kuma kiwon lafiyar jama’a. Sannan wurin ya zama matattarar batagari. A lokacin tsohon Gwamnan Legas Babatunde Fashola, ya ba mu aikin killace wajen tare da mayar da shi wajen da zai amfani al’umma maimakon cutar da su, a lokacin da aka ba ni aikin jama’a dadama ba su zata za mu iya ba.

Ita kanta gwamnatin ba ta dauka za mu iya sauya wajen cikin kankanen lokaci ba, sai da muka shafe sama da shekara guda muna aikin kwashe sharar wajen kafin a fara maganar ciko da kankaren da muka dora.

A lokacin kwashe wannan shara ce na gamu da wani abin mamaki, dama kamfanin wadansu ’yan kasar China ne suke ba mu manyan motocin kwashe sharar, to akwai wani lokaci muna tsakiyar kwasar sharar sai wani mutumin kasar China ya same ni ya ce, Alhaji yaya aka yi kuke sanya kudi kuna kwashe kudi kuna zubarwa a banza? Na ce ban fahimci me yake nufi ba, sai ya ce ai wannan shara da muke amfani da dukiya muna kwashe ta muna zubarwa ita ma dukiya ce. Nan take ya ba ni a rubuce irin na’urorin da za a yi amfani da su a saraffa sharar ta zamo dukiya wato takin gona na gargajiya da ake kira ‘Organic.’

Ya ba ni lissafin kudin da za a sayo injinan wannan abu shi ne ya sa yana fara tunanin kafa kamfanin yin taki a nan Kasuwar Abbatuwa, kuma yanzu haka shirye-shirye sun yi nisa mun yi magana da Kwamishinan Noma na Legas da sauran wadanda al’amarin ya shafa  inda muka yi kudirin fara samar da taki a nan Legas wanda za a rika kaiwa jihohinmu na Arewa inda muka fi yawan manoma ana sayar musu da shi cikin rahusa. Ka ga wannan hanya ce da za ta samar wa matasanmu ayyukan yi, za ta kuma kara dankon kyakkyawar alakar Legas da jihohin Arewa yadda ake kawo kayan  abinci daga Arewa za a rika kai taki Arewa daga nan Legas.

Kun kammala kwashe sharar, kun cike wajen har an dora gine-gine a kai, ko yaya aka kai ga haka?

Lokacin da aka ba ni aikin aiki ne da yake bukatar biliyoyin Naira, na yi yunkurin in nemi bashi daga banki abin ya faskara domin matsalar da ke tattare da tsarin bankunanmu a yanzu idan kana neman kudi ka yi abin arziki bankunanmu ba za su ba ka bashi ba, amma suna bai wa masu sayen motocin alfarma suna yin kashe-mu-raba da su.

A wancan lokaci na tafi Abuja na kawar da kadarorina da dama inda na tanadi kudi, sannan akwai abokina dan kabilar Ibo muka hada karfi da shi har Allah Ya ba mu nasara. Yanzu haka mun ci karfin aikin wajen a yanzu zai iya daukar manyan motocin tirela 250 da ke kawo shanu daga Arewa zuwa Kasuwar Abbatuwa. Sannan akwai manyan motocin da ke kai kayayyaki sassan Jihar Legas da su ma ke shigowa wannan waje suna tsayawa a nan.

Mun gina dakunan kwana na direbobi guda 85 da sito-sito guda 100 wadanda zuwa yanzu akasarin  ’yan kasuwa sun karba suna gudanar harkokinsu, har yanzu ana kan aikin, ka ga a baya matattarar shara da kazanta ce yanzu wajen ya zama kasuwa yana amfanar dubban jama’a wannan shi ne abin da muka sa a gaba tattalin arzikin kasa domin amfanin al’umma.

A baya-bayan nan Kungiyar ’Yan jarida ta Kasa ta ba ka lambar yabo, ko wannan na da alaka da aikin da ka yi na mayar da bola kasuwa?

Eh wannan abu haka yake a makon jiya, Kungiyar ’Yan jarida ta Kasa (NUJ) reshen Jihar Legas a karkashin jagorancin Shugabanta Dokta Kasim Olalere Akinreti, sun kawo min ziyara inda suka ba ni lambar yabo lura da wannan aiki da na yi. Suna sane da yanayin da wannan wuri yake  a baya, ganin yadda na sauya shi cikin karamin lokaci daga waje mai cutar da jama’a da gurbata muhalli ya koma mai amfanin al’umma da tara wa gwamnati kudin shiga. Wannan hobbasar da na yi ne dalilin da suka karrama ni. Dama haka abin yake duk aikin da ka yi jama’a na sane domin suna bibiyar al’amura, don haka abu mafi kyau shi ne mutum ya yi kokarin asassa alheri domin amfanin al’umma ta yadda ko ba ka nan za a amfana a kuma tuna da kai, haka ne ya sa muke ci gaba da jajircewa domin ci gaban al’umma.