✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muna so a ba ’yan Arewa mazauna Ogun kula a sabuwar gwamnati

Shugaban Kungiyar Hadakar ’Yan siyasa ’yan Arewa mazauna Jihar Ogun, Alhaji Usman Shehu Saffam ya nanata kudirinsu na ganin ’yan Arewa mazauna jihar sun amfana…

Shugaban Kungiyar Hadakar ’Yan siyasa ’yan Arewa mazauna Jihar Ogun, Alhaji Usman Shehu Saffam ya nanata kudirinsu na ganin ’yan Arewa mazauna jihar sun amfana da romon dimokuradiyya a sabuwar gwamnatin jihar da za a kafa cikin watanni biyu masu zuwa.

Ya ce a wannan karo ba za a mayar da ’yan Arewa saniyar ware ba kamar yadda aka yi musu a gwamnatin baya. “A baya mun mara wa gwamnati mai barin gado a karkashin jagorancin Gwamna Ibikunle Amosun amma da aka tashi kafa gwamnati ba a yi ta da jama’armu ba, don haka muka yanke shawarar mara wa zavavven Gwamna Dapo Abiodun baya kuma shi kansa yana sane da irin gudunmawar da muka ba shi. Ya kuma ba mu tabbacin samar wa matasanmu ayyukan yi, tare da bai wa mata jari da koya musu sana’o’in dogaro da kai. Sannan za mu cusa matasanmu a duk guraben da muke da tabbacin za su samu ci gaba a rayuwarsu, tun daga matakin mazavu da kananan hukumomi zuwa gwamnatin jihar,” inji shi.

Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da shugabannin ’yan Arewa masu yin siyasar APC suka shirya bikin nuna farin cikinsu ga nasarar zaven Dapo Abiodun, wanda ya yi takara a karkashin Jam’iyyar APC, bikin da ya gudana a ranar Lahadin da ta gabata a Unguwar Sabo Abeokuta, kuma ya samu halartar ’yan Arewa mazauna sassan jihar da suka hada da Ijebu-Ode da Ifo da Shagamu da Ogere da Ibafo da Karar Sheri da sauran sassan jihar.

A jawabin daya daga cikin shugabannin ’yan Arewa, Alhaji Bala DBB yaba wa iyaye mata ya yi wadanda ya ce sun nuna kwazonsu a sha’anin siyasar da ta gabata. Don haka ya yi kira da a tabbatar an saka mUsu da alheri.

A nasa vangaren, Alhaji Hamza Basi wanda ya wakilci Shugaban Karar Shanu ta Isheri, kira ya yi ga ’yan Arewa su ba da himma wajen sanya ’ya’yansu a makarantun boko domin a yanzu rayuwa ta sauya komai ba ya yiwuwa sai da ilimi, kuma ya yi kira a gare su da su zamo masu bin doka da oda.

Haka zalika ’yan Arewar sun karamma daya daga cikinsu wato Alhaji Halliru da Sarautar Sarkin Gidan Sabon Gwamna Dapo Abiodun, inda aka nada masa rawanin sarauta, wanda shi ne zai zamo mai yi wa ’yan Arewa iso a duk lokacin da suka bukaci ganin Gwamna.

A karshe, ayarin ’yan Arewar a karkshin jagorancin Alhaji Shehu Saffam ya ziyarci zavavven Gwamnan Jihar Ogun Dapo Abiodun a gidansa da ke Iperu a karshen makon jiya, inda suka taya shi murna suka kuma nanata goyon bayansu gare shi tare da yi masa fatan alheri. Shi kuma ya tabbatar musu da niyyarsa ta damawa da su a sabuwar gwamnatin da za a kafa. Kuma ayarin ya kai wa Sanatan Ogun ta Yamma, Tolu Odebiyi irin wannan ziyara, inda ya shaida wa Aminiya cewa zai maida hankali wajen gabatar da dokokin da za su bai wa mata da matasa kulawa.

“Ka san idan ka tallafa wa mace tamkar ka tallafi iyali ne. Don haka zan ba su kulawa ta musamman, zan kuma gabatar da kudirin da zai bai wa matasa damar samun guraben ayyukan yi.” inji Sanata Tolu Odebiyi.