Matasa Mazauna Jihar Legas sun koka kan yadda shigo da makamai ya zama ruwan dare a Najeriya, abin da yake haddasa aikata ayyukan taddaci a kasar baki daya, saboda haka suka bukaci gwamnati ta matsa kaimi wajen daukar kwakkwaran mataki na dakile shi.
Matasan da suka kira kansu kungiyar matasa masu neman wa matasa aikin yi a cikin kasa, sun yi wannan kiran ne a wajen taron manema labarai da suka kira inda suka bayyana cewa a binciken da suka gudanar, sun gano cewa ana yawan shigo da makaman ne ta ruwa domin bakin iyakokin Najeriya ta ruwa ba su da wadataccen tsaron da ya kamata.
Shugaban kungiyar, Comrade Umar Isma’il ya ce shigowa da makamai barkatai kuma da rashin tsaron da bakin iyakokin Najeriya ta ruwa ke fuskanta ya sa da yawan matasan da suka samu damar mu’amala da wadannan makamai suke aukawa cikin aikin ta’addanci.
Comrade Umar ya ce kungiyarsu tana bayar da shawarar gwamnati ta samar da sojoji ruwa da ake kira da Turanci ‘Merchant Naby’ kwatankwacin wadanda ake da su a kasar Kanada da Amurka da Ingila da wasu kasashen da suka ci gaba.
Comrade Umar ya ce yana da jin kwarin gwiwar cewa muddin aka samar da wadannan sojoji za a samar da raguwar shigowa da makamai cikin Najeriya ko ma a dakile lamarin baki daya, kana kuma ya samar da aikin yi ga matasa ko kuma al’ummar kasa, domin idan za a dauki wadanda za su yi wannan aikin, matasa su ne suka fi dacewa su yi shi.
Shi ma daya daga cikin shugabannin kungiyar, Comarade Ya’u Basula Zuru da yake tofa albarkacin bakinsa game da samar da wadannan sojojin, ya nuna ba kasashen da suka ci gaba kadai suke da su ba, hatta a wasu kasashen Afirka irin Afirka ta Kudu da Ghana suna da su, lamarin da ya sa suke samun rashin kwararar makamai a cikin kasashensu.
Ita ma Mis Maggi Kateiko, daya daga cikin shugabannin kungiyar, ta yi karin bayani kana wadancan sojoji na ruwa da cewa ba su da bambanci da kifi domin sukan kwashe kwanaki cikin ruwa domin gudanar da aikin ko-ta-kwana.
Ita kuwa Hajiya Fatima Altine, a tata shawarar cewa ta yi samar da sojojin ruwan zai kara wa masu saka hannun jari kwarin gwiwar shigowa Najeriya. “Muddin harkokin tsaro suka inganta, to da yawan ’yan kasashen waje za su yi ribibin shigowa cikin kasar nan domin samar da masana’antu, wanda hakan yana nufin karin samar da aikin yi ke nan, musamman ga matasa”, inji ta.
‘Muna so gwamnati ta matsa kaimi wajen hana shigo da makamai’
Matasa Mazauna Jihar Legas sun koka kan yadda shigo da makamai ya zama ruwan dare a Najeriya, abin da yake haddasa aikata ayyukan taddaci a…