✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muna so mu kawo canji a harkar Hip-Hop – FBHR BOYZ

FBHR BOYZ sanannun mawakan Hip-Hop ne a Jihar Kano. A tattaunawarsu da Aminiya sun bayyana cewa burinsu shi ne su kawo canji a harkar Hip-Hop…

FBHR BOYZ sanannun mawakan Hip-Hop ne a Jihar Kano. A tattaunawarsu da Aminiya sun bayyana cewa burinsu shi ne su kawo canji a harkar Hip-Hop a Najeriya.

Su wane ne a cikin FBHR BOYZ?

Ni sunana Mustapha Ahmad Gadanya, akwai kuma Ahmad Abdullahi AMD sai Isa Mika’il Isa wanda aka fi sani da Classik Dorayi.

Yaushe FBHR BOYZ suka fara harkokin Hip-Hop?

Mun kafa wannan hadakar ce a shekarar 2016. Duk da cewa mun dade muna yin wakoki a daidaikumu. Amma tunanin kafa wannan tafiya ya zo min ne bayan da na ga akwai bukatar mu hada kai da wadansu mawakan don kara bunkasa wakokinmu na Hip-Hop.  Mun yi tunani mun ga cewa duk abin da za ka yi shi da mutane da yawa yakan zama ya bayar da fa’ida fiye da wanda tunanin mutum daya ne. Kuma haduwar tamu tana bayar da kwarin gwiwa ga sauran mawaka da ke cikin tafiyar. Zai zama cewa ko da mutum ba ya son yi da zarar ya san akwai wadansu da za su yi tare za ki ga ya mike ya mayar da hankali shi ma ya yi.

Ba ma cikin mawakan da ba su waye ba wadanda ke yi wa junansu hassada. Mu mun fi so mu hadu a wuri guda don mu amfana da basirar juna. Waka wata hanya ce mai saurin isar da sako ga jama’a domin ta hanyar waka mukan fadakar da wa’azi . Wani kuma za ki ga ba zai saurari wa’azi ba amma zai saurari waka, to ta nan za ki ga ya wa’azantu ya kuma fadakantu.

Yaya kuke gudanar da wakokinku?

Yawanci idan tunanin waka ya zo wa daya daga cikinmu, to, zai sanar da saura cewa ga wakar da yake tunanin yi kuma ga takenta. To daga nan sai kowanenmu ya je ya rubuta baitoci a kan wannan wakar. Kasancewar muna da dokokinmu na rubuta waka kamar guje wa amfani da kalaman da ba su dace ba da sauransu, idan muka je muka rubuto sai mu je sutudiyo mu buga ba tare da mun yi gwaji ba. Kuma wani abu da zai ba ki mamaki sai ki ga kamar mutum daya ne ya rubuta.

Zuwa yanzu wakoki nawa kuka yi?

Wakokin da muka yi suna da yawa. Akwai irin su A daina Bleaching ’Yan mata da Lokaci Ne da Wai Ba Ta Sona da Ba Maraya Sai Rago da Zimalash da I am no one da Mata Iyayenmu da Zaurance da sauransu.

Mene ne burin FBHR BOYZ a wannan tafiya?

Gaskiya abubuwan namu da yawa, muna so mu kawo canji a harkar wakokin Hip-Pop a Najeriya gaba daya, tun daga kan amfani da kalmomi a wakokin da sanya sutura da kuma mu’amalar mawakan da masoyansu. Za mu canja tunanin mawaka ta hanyar gani daga gare mu. Muna so kuma idan muka kai inda muke so mu rika tallafa wa kananan mawaka masu tasowa da tallafin da ya kamata da kuma shawarwari da janyo su a jiki yadda su ma za su taso su samu karbuwa a wajen al’umma. Idan muka samu yadda muke so za mu rika shirya tarurrukan kara wa juna sani da na horarwa ga wadanda suke tasowa.

Kun taba samun tallafi daga gwamnati?

A gaskiya mawaka ba su samun tallafi daga gwamnati musamamn ma mawakan Hip-Hop. Ita gwamnati in dai ba wakokin siyasa za a yi mata ba, to ba ta kallon mawaka.

Da a ce mawakan Hip-Hop za su samu tallafi daga gwamnati na tabbata da wakokin sun ci gaba kuma da mutane da dama sun samu aikin yi. Ita kanta gwamnati da ta huta da batun sama wa al’umma aikin yi, domin ko a yanzu za ki tarar da kimanin mutum 10 a karkashin mawaki guda daya ba ya ga iyalinsa. Misali kamar yadda aka dauki ’yan fim aka kai su Indiya kamata ya yi a ce an kai mawaka ko kasashen waje ko ma a cikin kasar nan don su samu horo a kan harkar waka. Akwai bukatar gwamnati ta samar wa mawaka kayan aiki musamman sutudiyo yadda za a rika gudanar da ayyuka a wurin.

Mene ne sakonku ga masoyanku?

Muna godiya ga masoyanu da ke Kano gaba daya da kuma na Dorayi wadanda muka taso tare. Muna yi musu albishir cewa akwai wata kyauta babba da za mu yi musu ta sabuwar wakarmu mai suna Masoyanmu.