✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Murna ta sa iyaye sun manta jaririnsu a tasi

Jami’an ’yan sandan birnin Hamburg a kasar Jamus sun wallafa wani rahoto a kafar sadarwar zamani ta Facebook, inda rahoton ke cewa, wasu matasan ma’aurata…

Jami’an ’yan sandan birnin Hamburg a kasar Jamus sun wallafa wani rahoto a kafar sadarwar zamani ta Facebook, inda rahoton ke cewa, wasu matasan ma’aurata sun manta da jaririn da suka haifa a cikin motar tasi a hanyarsu ta komawa gida daga asibiti bayan haihuwa.

A cewar wasu rahotannin shafukan sada zumunta na zamani sun wallafa cewa iyayen da suka manta jaririnsu a tasi, haihuwar su ta biyu ke nan bayan dawowar su daga asibitin Hamburg yayin da suke cike da farin cikin samun karuwar iyali na kai wa adadin su hudu a gida. A lokacin da suke kokarin fitowa daga cikin tasin cikin annashuwa, sai suka manta suka bar jaririn suka tafi dan su dan shekara daya suka biya direban tasin, bayan tasin ta wuce sai suka ji kamar akwai wani abu da suka rasa, a lokacin da suka tuna sun rasa jaririn, lokaci ya riga ya kure masu.

Bayan mahaifin jaririn ya tabbatar da tasin ta wuce da jaririn sai ya bita da gudu da nufi zai dakatar da direban, amma abin ya cutura, sai ya fahimci abu mafi sauki shi ne ya tuntuvi jami’an ’yan sanda. Shi dai direban bai san iyayen sun manta da jaririn su a kujerar bayan motar ba, sai ya wuce kawai inda zaije cin abincin rana ya ajiye motar inda ake ajiye motoci. ’Yan sandan suka yi ta ci gaba da neman direban a birnin.

Bayan direban ya dawo daga cin abincin rana, sai ya nufi tashar jirgin sama don dauko wani fasinja, duk da yake ya yi tafiya mai nisa amma bai san akwai jariri a cikin motar ba, jaririn ya nata barci ba tare da ya yin kuka ba ta yadda direban zai fahimci akwai mutum a cikin motar, har sai da wani fasinja ya shiga cikin motar ta wurin kejerar baya sai ya sanarwa direban tasin abin da ya gani hakan yasa jaririn ya farka daga barcin ya fara kuka.

An yi nasarar direban tasin ya yi abin da ya dace ta hanyar tuntuvar jami’an ’yan sanda, daga nan suka umarci direban da ya ziyarci ofishin ’yan sandan, a nan ne iyayen jariri da jaririn suka hadu.

Direban ya ce, ”Na yi jimamin yadda iyayen jaririn  suka ji game da jiran sauraran rahoton inda jaririn yake, amma kuma har su iya mantawa da dan da suka haifa a cikin mota bayan haihuwa“.