Da Dumi Dumi

Murnar shiga Sabuwar Shekarar Musulunci ta 1441Bayan Hijira

An shiga sabuwar shekara a duniyar Musulunci, ta 1441 Bayan Hijirar Annabi Muhammad (SAW) daga Makkah zuwa Madina. Wannan kaura ita ce tushen assasa tarihin yin hijirar Manzon Allah (SAW) wadda ta faru a shekarar 622 Miladiyya, kuma daga nan ne tsarin lissafin Hijira na musulunci ya faro, wanda Halifa na Biyu, Umar Ibn Al-Khattab ya bullo da shi a shekara ta 638 Miladiyya ya kuma bullo da tsarin ne domin tabbatar da wasu muhimman lokuta da aka yi amfani da su a lokacinsa.

Umar (RA) ya tuntubi mashawartansa a kan wace rana ce, ya kamata ta kasance sabuwar shekara ga al’ummar Musulumi, inda dukkansu suka amince da cewa ranar da aka yi hijira ita ya kamata, an kuma zabi ranar ce bisa tsarin adadin kwanaki na shekara inda aka fara kirge daga baya, har ta kai ga ranar1 ga watan Al-Muharram, a matsayin ranar 1 ga Sabuwar Shekarar Musulunci, a kan takaita lamarin Hijira zuwa ga Bayan Hijira wadda aka amince cewa ita ce ta zama tushen kafa tsarin addinin Musulunci da kuma matsayin tarihinsa a fadin duniya.

Tsarin watannin Musulunci ya kunshi wata 12 da suka faro daga Muharram, Safar, Rabi’ul Awwal, Rabi’us Sani, Jimad Ula, Jimad Akhir, Rajab, Sha’aban, Ramadan, Shawwal, Zul-Kida da kuma Zul Hajji. Allah Mai girma da Daukaka Ya ce “Hakika adadin watanni a wajen Allah goma sha biyu ne, tun daga ranar da Ya halilci sammai da kasai, kuma daga cikinsu akwai hudu masu tsarki.(K:9:36)

Tunda tsarin watanin Musulunci ya ta’allaka ne a kan tsarin Musulunci, shi ne yake sa wa ake samun Kalandar Musulunci ta fi gajarta a kan ta Nasara da kusan kwana 11. Su watanni a Musulunci ba sa alakantuwa da wani yanayi, don haka ne ma dukkan bukukuwa na Musulunci suna zuwa ne a watan da aka saba yin su, sukan iya zuwa a wani lokaci na yanayi daban, Misali azumi da Aikin Hajji sukan iya zuwa a lokacin bazara ko sanyi, wanda sai bayan adadin shekara 33 ne yanayin yakan juya ya sake zuwa a daidai wannan lokaci.

Muhimmanci tsarin Kalandar Musulunci yana dogara ne a kan yin amfani da wasu muhimman tsare-tsare na Musulunci, misali azumin Watan Ramadan a kan fara shi a ranar  1 ga watan Ramadan, haka Aikin Hajji akan fara shi tun daga ranar 8 zuwa 13 ga watan Zul-Hajji, kazalika bukukuwan Sallar Idi Karama da Babba ana yin su a ranakun 1 ga watan Shawwal da kuma ranar 10 ga watan Zul-Hajji. Allah Mai girma da Daukaka Ya fadi a cikin Alkur’ani Mai girma cewa: “Suna tambayarka (Ya Muhammad) game da jaririn wata, Ka ce musu su abin kirgawar lokaci ne ga mutane da kuma aikin Hajji.’’(K:2:189).

ADVERTISEMENT

Farkon Sabuwar Shekarar Musulunci ya kamata ta kasance lokaci ne na nuna godiya ga Allah (SWT) hade da neman gafara da kuma sake zage dantse wajen bin koyarwar Annabi Muhammad (SAW). Da sake yin dubi a kan yadda ya bar mahaifarsa domin yada addinin Allah, wanda ya kamata kowane Musulmi ya zama mai yin koyi da irin hali na Manzon Allah (SAW) wajen bin gaskiya da kuma nuna kauna ga mabiya sauran addinai kamar yadda ya koyar a tsakanin mabiyansa.

Don haka muna kira ga Musulmi su ci gaba da yi wa kasar mu addu’a da kuma shugabanninmu a dukkan matakai da kuma Allah (SWT) Ya kawo mana dauki a kan halin da muka tsinci kanmu a ciki a wannan kasa, na kalubalen tsaro da ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane da sauran abubuwa da ke damun kasar nan. Da fatan Allah (SWT) don albarkar Annabi Muhammad (SAW) Ya kawo mana saukin wadannan al’amura.

Muna yi muku Barka da Sabuwar Shekara da fatan an shiga lafiya.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya