Da Dumi Dumi

Muryar Talaka ta karrama fitattun ’yan Najeriya

Kungiyar Muryar Talaka ta Kasa ta gudanar da taronta karo na 9  a garin Nguru a Jihar Yobe mai taken ‘Cimma Muradun Karni na Daya na Kawar da Talauci a Najeriya nan da shekara ta 2030,” inda ta karrama wasu fitattun mutane.

Shugaban Kungiyar ta Kasa, kuma Mai bai wa Gwamnan Jihar Kebbi Shawara kan Kafofin Yada Labarai na Zamani,  Malam Zaidu Bala Kofa Sabuwa Birnin Kebbi, ya ce kungiyar ta kafu ne domin kare ’yancin talaka inda gidajen rediyon kasashen waje irin Muryar Amurka da BBC da Rediyon Faransa da Muryar Jamus (DW) suke ba su damar aikewa da sakonninsu.

Ya ce sun gudanar da taron farko ne a garin Malumfashi, Jihar Katsina, su bakwai inda suka tattauna yadda za su kafa kungiyar.

Ya ce cikin irin aikace-aikacen kungiyar ke yi suka bankado aika-aikar rashin imanin da aka yi wa wani almahajiri mai suna Nafi’u a garin Bajoga helkwatar Karamar Hukumar Funakaye a Jihar Gombe, inda suka tsaya masa har sai da hukuma ta shiga batun.

Mai masaukin baki kuma Shugaban Kungiyar ta Jihar Yobe, Kwamared Salisu Armaya’u Nguru, ya ce sun dauki nauyin taron ne a Nguru saboda su tabbatar wa ’yan Najeriya cewa Jihar Yobe yanzu ana zaman lafiya ba kamar yadda wadansu ke ganin har yanzu jihar na fama da matsalar tsaro ba.

ADVERTISEMENT

Wakilin Gwamnan Jihar, Kwamishinan Ilimi, Dokta Sani Idris, ya ce Gwamna Mai Mala Buni, mai tausayin talakawa ne shi ya sa ya turo shi ya wakilce shi a wannan taro na Muryar Talaka.

A lokacin taron an karrama Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan da Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni da Sakataren Gwamnatin Jihar da manyan alkalai da shahararren mawakin siyasan nan, Dauda Kahutu Rarara.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya