✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Musa Fagen Gawo ne ya lashe zaben fid-da-gwani na APC a mazabar Garki da Babura

Wakilai masu zaben wanda zai tsaya takara a Jam’iyyar APC 688 ne suka yi zaben fid-da-gwani na kujerar Majalisar Wakilai da aka gudanar a Karamar…

Wakilai masu zaben wanda zai tsaya takara a Jam’iyyar APC 688 ne suka yi zaben fid-da-gwani na kujerar Majalisar Wakilai da aka gudanar a Karamar Hukumar Babura a ranar Litinin da ta gabata a sakatariyar karamar hukumar                                                                                                                                            An fara zawarcin kujerar ce sakamakon rasuwar wanda ke kant Alhaji Muhammad Adamu Fagen Gawo wanda ya rasu a ranar31 ga Disamban bara a Dubai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa.

Rasuwarsa ta ba masu neman kujerar damar fitowa a dama da su, ciki har da ’ya’yansa uku, Musa Muhammad Adamu Fagen Gawo da Aliyu Muhammad Adamu Fagen Gawo da Sunusi Muhammad Adamu Fagen Gawo Wanda a ranar Lahadi ya shaida wa uwar  jam’iyyar ta Jihar Jigawa cewa ya janye ya bar wa kanensa Aliyu Muhammad Adamu Fagen Gawo. Sai Musa Laila Dogon Yaro da Injiniya Idris Muhammad Zangi, wanda shi ma ya janye daga takarar a ranar zaben inda ya ce yana tunanin ba za a yi masa adalci ba.

An gudanar da zaben a gaban jama’a tare da manyan jami’an tsaro da manyan ’yan siyasar yankin Babura da Garki

An  fara zaben da misalin karfe 1:00 na rana aka kammala jefa kuri’a da misalin karfe 5:00 na yamma kuma wakilan Jam’iyyar APC na Kasa da suka hada da Alhaji Muktari Shehu Jibrin da abokan tafiyarsa sun tabbatar da cewa a cikin ’yan takarar Alhaji Musa Muhammad Fagen Gawo.ne ya lashe zaben da kuri’a 547, yayin da dan uwansa Aliyu Muhammad Adamu ya samu kuri’a 32, shi kuma Malam Idris Zangi Muhammad ya samu kuri’a 21.

Wakilan Jam’iyyar APC da suka zo daga Abuja sun tabbatar wa Alhaji Musa Muhammad Adamu a matsayin wanda ya lashe zaben inda zai tunkari abokan karawarsa da za su fito daga sauran jam’iyyu a zaben da za a gudanar a  ranar 14 ga watan Maris mai zuwa.