✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Musulmi da Kiristoci sun yi bikin Hawan Daushe a Kafanchan

Bikin Hawan Daushe da aka saba gudanarwa duk washegarin ranar Sallah ya zo da sabon salo a Masarautar Jama’a da ke Jihar Kaduna inda da…

Bikin Hawan Daushe da aka saba gudanarwa duk washegarin ranar Sallah ya zo da sabon salo a Masarautar Jama’a da ke Jihar Kaduna inda da Musulmi da Kiristoci suka hadu a fadar Mai martaba Sarkin Jama’a Alhaji Muhammad Isa Muhammad II da ke garin Kafanchan tare da masu raye-rayen gargajiyarsu, abin da aka ce fiye da shekara ashirin ke nan rabon da ganin haka.

Kamar yadda aka saba, a kowace shekara Sarkin da ayarinsa da ya kunshi mahaya dawaki da masu tafiya a motoci da babura da kekuna da kuma masu takawa a kafa kan yi tattaki daga Kofar Fadar Sarkin zuwa Babban Asibitin garin domin gayar da marasa lafiya tare da yi musu addu’a.

A wannan karon, baya ga gudumnmawar kudi da Sarkin da ayarinsa suka bayar a asibitin, Sarkin ya mika wa shugaban asibitin da gudunmawar katan-katan na wasu magunguna don tallafa wa marasa lafiyar da ke kwance a asibitin.

Lokacin da yake jawabi a asibitin, Sarki Muhammad Isa Muhammad ya bayyana godiyarsa ga Allah kan kammala azumin Ramadan lafiya tare da yin kira ga al’umma su yi amfani da darussan watan azumi tare da rungumar zaman lafiya.

A jawabin Babban Daraktan Asibitin, Dokta Samuel Kure Maidawa ya mika godiyarsa ga Sarkin bisa ga irin nuna damuwarsa ga marasa lafiya a lokacin da wadansu takwarorinsu da ’yan uwansu ke gidajensu suna shagulgula.

Dokta Kure, ya ce irin wannan dabi’a ta Sarkin, wadda ya gada tun iyaye da kakanni tana matukar burge shi inda ya yi fatar alheri da tsawon kwana ga Sarkin da kuma fatan samun dawwamammen zaman lafiya mai dorewa a yankin da jihar.

Bayan kammala ziyarar ce Sarkin da jama’arsa da sauran baki suka bi ta Layin Zariya suka dawo babban titin garin kafin inda su koma kofar fada don ci gaba da bukukuwan.

Daga cikin manyan bakin da suka yi jawabi akwai shugabannnin kananan hukumomin Jama’a da Kaura da wakilin Mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna, Hajiya Hadiza Balarabe, wanda mjinta, Alhaji Lamido Balarabe Dangaladiman Jama’a da ya fito zuriya daya da Sarkin Jama’a, ya wakilta.

Lokacin da yake jawabi, shugaban Karamar Hukumar Sanga, Mista Charles Danladi ya taya Sarkin da sauran al’ummar Musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan lafiya, inda ya yi fatan samun zaman lafiya da karin dankon zumunci a tsakanin kananan hukumomin Sanga da Jama’a wadanda a baya suke tare a Karamar Hukumar Jama’a.

Kuma kamar yadda aka hadu Musulmi da Kiristoci don taya Musulmi bukukuwan Sallah yana fatan za a taya su sake haduwa a bukukuwan Kirsimeti a watan Disamba mai zuwa.

Alhaji Lamido Balarabe, Dangaladiman Jama’a, wanda kuma shi ne babban bako a wajen ya ba da hakuri kan rashin kasancewar mai dakinsa wadda ita ma ’yar gida ce a masarautar saboda wani aiki da ya taso inda Gwamnan Jihar ya bukaci ya wakilce ta.

Dangaladiman, wanda ya nuna farin cikinsa kan yadda aka gudanar da bikin Sallar lafiya da kwanciyar hankali, ya yi fatan nan gaba a ci gaba da yadda ake Hawan Daushen a shekarun baya da ake zuwa har masaukin manyan baki (BIP) na karamar hukumar don ganawa da Shugaban Karamar Hukumar tare da yin liyafa a can wanda aka dauki shekaru masu yawa da dainawa saboda matsalar tsaro.

A lokacin da yake nasa jawabin, babban mai masaukin baki kuma shugaban Karamar Hukumar Jama’a, Mista Peter Danjuma Aberik ya nanata kira ne kan zaman lafiya inda ya ce ko wuraren da suka ci gaba ne sukan sulmuyo kasa idan suka rasa zaman lafiya ballantana inda suke tatata.

“Ina kira ga jama’a su guji yada jita-jita da kalmomi na batanci ko na harzuka wadansu a kan addini ko kabila ko siyasa. Yanzu ba lokacin siyasa ba ne tunda an gama zabubbuka don haka a hada kai a tafi tare a tsira tare,” inji shi

A karshe ya jinjina wa Sarkin Jama’a a kan irin kokarin da yake yi wanda hakan ya sa yankinsa ya samu zaman lafiya na tsawon lokaci, sannan ya jinjina wa Gwamnan Jihar Kaduna bisa ga hadin kan da yake ba su don dorewar zaman lafiya.

Bikin na bana ya samu halartar kungiyoyin makada da mawaka da suka hada da ’yan kabilar Koro da ’yan rawar kwarya daga Karamar Hukumar Kagarko da makadan kabilar Numana da ’yan rawar baya daga Karamar Hukumar Sanga da na kabilun Ibo da Yarbawa da Dankwairon Giwa da masu busa algaita da sauransu, inda suka nishadantar da mahalarta taron, tare da dada nuna irin yadda zaman lafiya ya samu a yankin.