✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Musulmin Awi a Jihar Kuros Riba na bukatar gudunmawa

Al’ummar musulmi mazauna garin Awi a karamar Hukumar Akamkpa ta Jihar Kuros Riba sun bukaci ilahirin musulmi su taimaka musu da kudi da kuma kayan…

Al’ummar musulmi mazauna garin Awi a karamar Hukumar Akamkpa ta Jihar Kuros Riba sun bukaci ilahirin musulmi su taimaka musu da kudi da kuma kayan gini domin su gina masallacin Juma’a da makarantar Islamiyya da kuma fitar da makabarta a filin da suka saya.
Limamin masallacin garin, Malam Abudllahi Yakub ne ya bukaci haka a hirarsu da Aminiya a makon da ya gabata, inda ya yi nunin sun sayi filin, “Amma muna neman cikon kamar Naira dubu dari biyar domin kudin hannunmu ba su kai adaddin mu kammala biya ba”.
Limamin ya bukaci duk wadanda za su taimaka su bayar da taimakon ga sarkin Hausawan Awi ko Limamin masallacin ko kuma su aika da kayan aiki, domin har sun sami sukunin fara gina masallaci. “A yanzu wucin-gadin gini muke ibadarmu, akwai bukatar mu mayar da gini, kasancewa ana samun karuwar jama’a musulmi da ke zuwa harkokin kasuwanci ko aikin gwamnati.
Yankin Akamkpa ya kunshi garuruwan Mbarakom da Netun da Awi, wanda ke da musulmi ’yan asalin Kuros Riba da ma wasu ’yan salin arewacin kasashen Afirka.
Ya yi fata jama’a za su taimaka masu, musamman ma da kayan gini domin ci gaba da aikin.