Da Dumi Dumi

‘Musulmin Cross River za su koma ibada kamar yadda suka saba’

Gwamna Ben Ayade na jihar Kuros Riba

Alummar musulmin Kuros Riba sun cimma matsaya tsakanin su da gwamnatin jihar a kan yadda za su ci gaba da gudanar da addininsu kamar yadda aka saba.

Hakan ya biyo bayan tattaunawa tsakanin Alhaji Tanimu Hassan, mataimaki na musamman a kan addinin Musulunci ga gwamnan jihar Farfesa Ben Ayade, da mataimakin gwamnan jihar Farfesa Ivara Esu, ganin cewa a karshen wannan mako ake sa rai a yi Karamar Sallah.

Alhaji Hasan ya shaida wa Aminiya cewa, “Mun tattauna da mataimakin gwamna yanzu, mu Musulmi za mu ci gaba da yin salloli a masallatai kamar yadda aka saba”.

Mataimaki na musamman kan addinin Musulunci ga gwamnan ya ci gaba da cewa “ko wanne masallaci kada ya haura mutum dari biyar.

“Kuma kowa zai sa takunkumin rufe fuska, a ajiye ruwa da kayan wanke hannuwa a waje”.

ADVERTISEMENT

Da aka tambaye shi game da Sallar Idi da ta Juma’a sai ya ce, “an bar mu mu yi Sallar Idi amma dokar bari a yi Sallar Juma’a za ta fara aiki daga 24 ga watan nan”.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya