✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Musulmin Siriya da Masar na fama da wahala a lokacin Ramadana

Musulmin duniya sun fara azumin watan Ramadana, musaman a Gabas ta tsakiya inda Musulmi ke fama da mawuyacin hali a kasashen Siriya da Masar, inda…

Musulmin duniya sun fara azumin watan Ramadana, musaman a Gabas ta tsakiya inda Musulmi ke fama da mawuyacin hali a kasashen Siriya da Masar, inda ake fama da tarzoma da kuma yaki. Duk da wannan matsalar mafi yawancin Musulmin duniya a ranar Laraba suka far aazumi.
A Hadaddiyar Daular Larabawa, wasu daga cikin sarakunan masaratun Abu Dhabi da Dubai da Fujaira da Ra’asul Khaimah (RAK), sun yafe wa wasu fursunonin zaman wakafi. Suna kashe dimbin kudi don buda baki da ciyar da marasa galihu. Uwa-uba an rage lokutan aikace-aikace a ofisoshin gwamanti da na kamfanoni msu zaman kansu.
Tuni aka fara tafsirin Alkur’ani da wa’azi da sallar tarawihi a kasashen Larabawa da sauran sassan duniya inda Musulmi ke da yawa.
Yakin basasar Siriya ya salwantar da rayukan mutanen da yawansu ya kai dubu 93. A rahoton Majalisar dinkin Duniya, darajar kudin kasar ya fadi, ga kuma tsadar rayuwa. Faduwar Gwamnatin Mursi ta haifar wa Masar matsalolin da suka hada da karyewa darajar kudin kasar da kashi 22 cikin 100; sannan kasar na fama da amtsar makashi. Yanzu haka Hadaddiyar Daular Larabawa ta UAE na shirin bai wa kasar rancen Dalar Amurka uku, a daidai lokacin da ta aike mata da tallafin ton dubu 30 na iskar gas.