✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutane sun ki yarda da mai unguwar da aka nada musu a Adamawa

Mutanen Unguwar Sukur da ke Karamar Hukumar Madagali a Jihar Adamawa sun ki yarda da sabon mai unguwa Mista Ijarafu Bayal da aka nada musu.…

Mutanen Unguwar Sukur da ke Karamar Hukumar Madagali a Jihar Adamawa sun ki yarda da sabon mai unguwa Mista Ijarafu Bayal da aka nada musu.

Shugaban Ci-gaban Unguwar Sukur, Mista Tom Kami ne ya bayyana haka a ranar Lahadin da ta gabata inda ya ce mutanen unguwar ba su amince da wannan nadin na mai unguwa ba.

Ya ce mutanen Unguwan Sukur sun riga sun zabi Mista Markus Ezra wadda shi ne dan marigayi mai unguwa Rabaran Ezra Makarma domin ya gaji mahaifinsa.

Tom ya ce sun yi matukar mamakin yadda Gwamna ya dauko wani daga wata kabila daban ya ba shi mukamin.

Ya yi kira ga gwamnati ta yi musu adalci sannan ta cire sabon mai unguwa kasancewar ba kabilansu daya ba.

Ya ce wannan mataki da Gwamna ya dauka zai iya janyo  tashin hankali a wannan bangaren wadda bai dade da suka yi sulhu a tsakaninsu.

“A dauko wata kabila sannan a ce ta shugabance mu, gani nake ba a yi mana adalci ba kuma wannan ba adalci ba ne. Wannan aikin ganganci ne da aka yi domin wulakanta mutanenmu wadanda su ne na farko a Afirka da kuma na 25 a duniya wajen taron farko na UNESCO, “inji shi.

Ya kara da cewa, “Mutanenmu na ganin mukamin mai anguwa a matsayin hanya ta ganawa da Gwamna. Adalcin da za a yi mana shi ne kawai a dauko dan tsohon mai unguwa ya gaji mahaifinsa domin samun ci gaba da kuma kwanciyar hankali.”

Kakakin Gwamnan Jihar Adamawa, Mista Solomon Kumangar ya ce an amince da sabon Mai unguwar Sukur ne tun lokacin Gwamna Muhammadu Bindow.

Ya ce ya yi mamakin yadda wadansu ke tada hankalinsu game da wannan sabon mukami inda ya ce yin hakan zai jayo ci-baya ne a tsakaninsu maimakon zaman lafiyar da aka san su da shi.

Ya kara da cewa zabe aka gudanar a unguwan sannan Bayal ya fi Ezra da kuri’u don haka shi ya cancanci wannan mukami.

A halin yanzu dai dattawan garin sun yi kira a yi sulhu a tsakanin mutanen Sukur da na Madagali.