✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutane sun mutu, gidaje 600 sun rushe bayan iska mai karfi a Kano

Mutun shida sun rasu baya ga gidaje 600 da suka rushe kasamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da iska mai karfi a kananan hukumomi…

Mutun shida sun rasu baya ga gidaje 600 da suka rushe kasamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da iska mai karfi a kananan hukumomi hudu a jihar Kano.

Kazalika wasu mutum 1,752 sun rasa muhallansu sakamakon iftila’in a cikin mako guda a jihar, inji Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Kano.

Shugaban hukumar Sani Jili ya ce wutar lantarki ta kashe daya daga cikin mamatan, sauran biyar din kuma gini ne ya fada a kansu.

Sani Jili ya ce iftila’in ya shafi Kananan Hukumomin Gwale, Gwarzo Rimin Gado, da kuma Kibiya ne a cikin a makon jiya.

Ya ce hukumarsa na jiran rahoton sauran kanana hukumomin da abin ya shafa yayin da ma’aikata ke kokarin tattara alkaluman barnar da aka samu.

A cewarsa Rimin Gado da Kibiya sun riga sun gabatar da rahotanninsu, har an tallafa musu da kayan rage radadi a matakin farko ga wadanda suka yi asara.

Kaya da aka raba wa mutanen kai tsaye sun hada da “kayan abinci, tufafi da kayan shinfida, sai kuma buhunan siminti”, inji shi.