✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutanen da aka ceto sun bayyana yadda aka yi garkuwa da su

A farkon makon nan ne Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna ta tabbatar da garkuwa da wadansu mutum shida a hanyar Abuja zuwa Kaduna. Rundunar ta ce…

A farkon makon nan ne Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna ta tabbatar da garkuwa da wadansu mutum shida a hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Rundunar ta ce an yi garkuwa da mutanen ne ranar Lahadin da ta gabata da misalin karfe 10 na dare.

Sannan jami’an tsaron sun sanar da nasarar kubutar da mutanen daga wajen masu garkuwa da su ne a shekaranjiya Laraba.

Da suke yi wa Aminiya bayanin yadda lamarin ya faru, mutanen wadanda suka fito daga garin Offa a Jihar Kwara sun ce wadanda suka sace su ba su yi musu fyade ko cin zarafinsu ba amma sun azabtar da su a kwana uku da suka yi a hannunsu.

Mutanen da suka kunshi mata uku da maza uku sun ce an azabtar da su da duka da yunwa da kishin ruwa

Sojoin Najeriya ne suka yi nasarar ceto su daga cikin dajin Rijana a wani samame da suka kai sansanin masu garkuwa da mutanen da safiyar shekaranjiya Laraba.

Daya daga cikin matan da aka yi garkuwa da su, A’ishat Aliyu Bisola ta ce wadanda suka yi garkuwa da su Fulani ne kuma suna sanye ne da kayan sojoji a daren da suka tare su a kan hanyarsu ta zuwa Kaduna.

“Da suka tare mu suna sanye ne da kayan sojoji daga nan suka wuce da mu cikin daji sai da muka yi tafiyar sa’a uku cikin daji kafin muka kai sansaninsu da ke saman wani tsauni. A nan suka ajiye mu suka ce sai an biyasu Naira miliyan 10 kafin su sake mu.

Da gari ya waye, wato ranar Litinin sai suka rage kudin zuwa Naira miliyan biyar. A ranar Talata bayan sun lura iyayenmu ba su da wannan kudi sai suka ce sun rage a kawo musu Naira miliyan biyu. Amma ba su yi mana fyade ba, sai dai sun rika dukanmu da kuma azabtar da mu ta hanyar hana mu abinci da ruwansha,” inji ta.

Ita ma Khadija Kehinde Okunola ta ce babu wacce aka yi wa fyade a cikinsu sai dai kawai sun sha duka.

“Abin da kawai suke mana shi ne duka tare da matsa mana cewa a kawo musu kudi. Domin su wai kudin kawai suke so. Amma ba su yi mana fyade ba. Kuma ba su bugi karamar kanwata da ke tare da mu ba a cikin dajin,” inji ta.

’Yan matan sun kuma bayyana wa Aminiya cewa a lokacin da sojojin suka isa dajin suka fara harbi sai ’yan ta’addan suka gudu cikin daji suka bar makamansu da harsasai domin gudun kada a kama su.

Bayan da sojojin suka ceto su, sai aka mika su ga Gwamnati Jihar Kaduna, sannan gwamnatin ta sa a kai su asibiti domin duba lafiyarsu kafin a mika su ga shugabanin Kungiyar Al’ummar Offa mazauna Jihar Kaduna.