✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutanen Sanga sun taya ’yarsu murnar takarar Mataimakiyar dan takarar Gwamna

’Yar takarar Mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna, Hajiya Hadiza Sabuwa Balarabe ta yi kira ga jama’ar karamar hukumarta ta Sanga su fito su kada wa Gwamnan…

’Yar takarar Mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna, Hajiya Hadiza Sabuwa Balarabe ta yi kira ga jama’ar karamar hukumarta ta Sanga su fito su kada wa Gwamnan jihar kuri’arsu don nuna godiya gare shi bisa bai wa ’yarsu matsayin da ba su taba mafarkin samu ba.

Hajiya Hadiza ta yi wannan kira ne a wajen walimar da jama’ar Karamar Hukumar Sanga suka shirya mata don taya ta murnar daukarta da Gwamna El-Rufa’i ya yi don ta rufa masa baya a zaben badi, inda Musulmi da Kiristocin garin baki daya suka fito don taya ta murna.

Bikin wanda aka shirya a garin Gwantu, hedikwatar Karamar Hukumar Sanga, ya samu halartar sarakunan Fadan Ninzo da na Gwantu da na Fadan Ayu da Sarkin Jama’a.

“Kun sani a baya ba a damawa da mutanen Sanga. To amma yanzu ya zama wajibi mu fito mazanmu da matanmu don yi da wanda yake yi da mu. ’Yan uwana mata da muke korafi ba a damawa da mu yanzu ga dama ta samu, baya ga kasancewata ’yar Sanga kuma in mace ce,” inji ta.

Shi ma da yake nasa jawabin, Sarkin Gwantu (Etum Gwantu) Janar Ilya Yamma (mai ritaya) ya yi kira ga matasa su guji shaye-shaye su kama hanyar neman ilimi domin a cewarsa, Hajiya Hadiza ta samu daukaka ce saboda karatun da ta yi wanda shi ke taimakonta har zuwa yanzu.

A karshe Mai martaba Sarkin Jama’a, Alhaji Muhammad Isa Muhammad II wanda kani ne a wajenta ya yi magana ne a madadin mahaifi da dangin Hajiya Hadiza gaba daya, inda ya mika godiyarsa ga Gwamnan jihar, bisa wannan karamci da ya yi musu.