Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Mutum 1 da shanu 4 sun rasu a hadarin tirela

Wani mutum da kuma shanu hudu sun rasu a wani mummunan hadarin mota da ya auku a gab da shataletalen Lugard Hall a tsakiyar garin  Kaduna.

Hadarin ya auku ne da misalin karfe 12 na dare ranar Talatar da ta wuce inda tirelar dauke da shanun ta fadi lokacin da direbanta ke kokarin wuce shataletalen.

ADVERTISEMENT

Aminiya ta samu bayanin cewa mutum daya ne ya rasu a asibiti yayin da mutum biyu kuma suka samu sauki.

Wakilinmu ya ce har zuwa shekaranjiya Laraba mattatun shanun na watse a gefen titi inda sauran dake a raye ke gefe guda.

ADVERTISEMENT

Wani da ke kusa da wurin da abin ya faru ya shaida wa Aminiya cewa direban saboda bako ne bai lura akwai shataletale a wurin ba.

Mataimakin Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadarurruka ta Kasa, Salisu Umar Galadanci ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Ya shawarci direbobi su kauce wa yin tafiyar dare.