✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 10,000 sun kamu da ciwon daji cikin wata guda a Najeriya

Alkaluma sun nuna yadda ake ci gaba da samun mutane ke kamuwa da cutar a kasar nan.

Akalla mutum 10,000 ne suka kamu da ciwon daji tun farkon wannan shekarar, kamar yadda uwargidan Gwamnan Jihar Kebbi, Zainab Shinkafi Bagudu ta bayyana.

Ta bayyana haka ne a ranar Alhamis a Abuja, yayin kaddamar da littafinta mai suna ‘Footprints’, First Ladies Against Cancer (FLAC).

Ta buga misali da Hukumar Bincike Kan Ciwon Daji (IARC) ta GLOBOCAN kan yadda alkaluman cutar ke kara hauhauwa.

Ta bayyana cewa littafin ya kunshi dukkan ayyukan FLAC da kokarin cike gibin kula da cutar daji a Najeriya.

Ta kuma jaddada bukatar magance halin ko-in-kula da ake nuna wa kan ciwon daji ta hanyar kara wayar da kan jama’a, hadin gwiwa mai dorewa da samar da tallafi da zai taimaka wajen rage tsadar magunguna.

Babban Daraktan Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Kasa (NPHCDA), Faisal Shuaib, ya ce Gwamnatin Tarayya za ta bullo da allurar rigakafin cutar a cikin jadawalin rigakafi na yau da kullun da za a ke yi a kasar nan a wannan shekara.

Allurar rigakafin ta HPV na taimakawa wajen yakar ciwon dajin mahaifa, wanda shi ne nau’in ciwon daji na biyu da aka fi samu a mata a yankin Kudu.

hu’aib, ya ce hukumar ta zage damtse wajen samar da allurar rigakafin ciwon hanta a Najeriya domin kare mutane daga kamuwa da cutar.

Ministan Lafiya, Osagie Ehanire, ya shawarci ’yan Najeriya da su guji gudanar da salon rayuwar da zai haifar musu da kamuwa da ciwon daji.

Ya kara da cewa Gwamnatin Tarayya za ta aiwatar da rigakafin cutar zazzabin cizon sauro a bana.