✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 13,106 ne suka warke daga COVID-19 a Legas —NCDC

Cibiyar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa (NCDC) ta ce zuwa yanzu mutum 13,106 ne suka warke daga cutar COVID-19 a jihar Legas. NCDC a shafinta…

Cibiyar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa (NCDC) ta ce zuwa yanzu mutum 13,106 ne suka warke daga cutar COVID-19 a jihar Legas.

NCDC a shafinta shafinta na Twitter ranar Talata ta ce ta samu alkaluman ne bayan hada adadin mutanen da suka warke bayan sun samu kulawa daga gida da kuma cibiyoyin kulawa da cutar a jihar.

NCDC ta ce yanzu Birnin Tarayya Abuja ya zarce jihar ta Legas a yawan masu dauke da cutar da ba su kai ga warkewa ba.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce a nahiyar Afirka akalla mutum dubu 957 ne suka kamu da cutar, sama da dubu 610 suka warke yayin da sama da dubu 20 kuma suka riga mu gidan gaskiya.