✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 17 da aka kama sun fallasa yadda suke aikata miyagun ayyuka a Jihar Oyo

Wadansu mutum 17 da ’yan sanda suka kama su bisa zargin aikata miyagun ayyuka a Jihar Oyo, sun yi bayanin yadda suke aikata danyen aikinsu.…

Wadansu mutum 17 da ’yan sanda suka kama su bisa zargin aikata miyagun ayyuka a Jihar Oyo, sun yi bayanin yadda suke aikata danyen aikinsu.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Oyo Mista Shina Olukolu shi ne ya nuna mutanen gungu-gungu ga ’yan jarida inda kowanne ya bayyana irin laifin da ya aikata.

Wadansu Fulani shida suna daga cikin mutum 17 da aka kama. Kuma an kama su ne dauke da bindigogi harba-ka-ruga guda 6 da suke amfani da su wajen aikata fashi da makami a kan hanyar Kishi zuwa Igbeti.

Jagoran Fulani makiyayan mai suna Salihu Ibrahim ya yi wa Aminiya bayani cewa, “Gaskiya ne an kama mu da wadannan bindigogi guda 6 amma duka ba sa aiki muna tsoratar da mutane da bindigogin ne mu karbi kudade daga hannansu kafin asirinmu ya tonu. Mu ne muka jefa kanmu cikin halin da muke ciki.”

Su kuwa Taiwo Salami da Kamarudeen Amusat an kama su ne kan zargin watsa wani magani na tsafi ga wata mata mai suna Mary Ajayi wanda ya kawar da hankalinta zuwa maboyarsu a Ibadan inda suka lalube ta suka kwashe mata Naira miliyan daya da dubu 400 da aka aike ta ta zuba a asusun banki. A lokacin da aka kama su an same su da karamar mota kirar Toyota Camry da suka tabbatar cewa, sun saye ta ce da wasu kayayyaki daga kudin da suka kwace daga matar.

Taiwo Salami ya shaida wa Aminiya cewa. “A lokacin da na kalli wannan mata sai na ga alamar akwai kudi tare da ita, sai kawai na rika bin sawunta na yi mata sihirin da ya kawar da hankalinta ta rika bi na har zuwa Unguwar Inalende inda na boye ta a cikin wani daki a wani rusasshen gida na lalube aljihunta na kwashe kudin. Mun yi lalata da ita wadda ta haifar da samun raunuka a sassan jikinta. Muna cikin kokarin kashe ta da yin tsafi da sassan jikinta sai asirinmu ya tonu aka kama mu.”

Kwamishinan ’Yan sanda Shina Olukolu wanda yake tare da Mataimakinsa Attahiru Isa, ya ja kunnen mambobin Kungiyar Direbobi ta NURTW da kada su kuskura su koma ga gudanar da kowane irin aiki musamman karbar kudade a tashoshin mota a fadin jihar domin yin haka haramtacce ne gare su. Ya tabbatar da cewa, za su ci gaba yin aikin tsaron lafiyar al’ummar jihar kamar yadda Sufeto Janar na ’Yan sanda Muhammed Abubakar Adamu ya umarce su.