Da Dumi Dumi

Mutum 17 sun rasu a wani harin bam a Somaliya

Wurin da bam ya tashi a qasar Somaliya
Wurin da bam ya tashi a qasar Somaliya

A kalla mutum 17 ne suka mutu a wani harin bam da ya tashi a cikin mota a birnin Mogadishu na kasar Somaliya.

Daraktan Babban Asibitin Mogadishu, Dokta Mohammed Yusuf, ya ce an kai karin wadansu mutum 28 da suka ji mummunan raunuka zuwa asibitin.

Fashewar ta auku ne a lokacin da wani dan kunar bakin waken da ake zargi ya tada bam din a kofar shiga wani otel da ke kusa da wata mahada da ake kira K-4 wadda take da yawan hada-hada a Mogadishu.

Shaidu sun bayyana cewa dan kunar bakin waken ya juya bayan motar ta kalli shingen duba ababen hawa na jami’an tsaro da ke kan hanyar da za ta kai ga filin jirgin saman kasar inda ya tada bam din.

Tuni dai kungiyar Al-Shabab ta dauki alhakin kai harin.

ADVERTISEMENT
Share