✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 1,740 sun yi ritaya bana a Jigawa

A bana mutum 1,740 ne suka ajiye aikin gwamnati a Jihar Jigawa, lamarin da ya sa wadansu ke tunanin wata rana za a wayi gari babu…

A bana mutum 1,740 ne suka ajiye aikin gwamnati a Jihar Jigawa, lamarin da ya sa wadansu ke tunanin wata rana za a wayi gari babu kwararrun ma’aikata saboda dukkan wadanda za a dauka aiki nan gaba ba za su samu horo daga wajen wadanda suka goge a fagen aikin gwamnatin ba.

Kamar yadda bincike ya nuna, daga watan Janairun zuwa  Disamban bana, ma’aikata 1,740 ne suka ajiye aiki yayin da Gwamnatin Jihar Jigawa ta kashe Naira biliyan 7 da miliyan 684 da dubu 173 da 536.04, kan fansho da garatuti kamar yadda Sakataren Hukumar Biyan Fansho da Garatuti na Jihar Jigawa Malam Hashimu Ahmed Fagam ya fadi lokacin da ya kira taron manema labarai a ranar Litinin da ta gabata.

Da yake karin bayani ya ce a watan nan na Disamba sun biya mutum 96 a matakin ma’aikatan jiha kudinsu da ya kama Naira miliyan 206, da dubu 164.

Yayin da a matakin kananan hukumomi suka biya mutum 108 hakkokinsu da suka ajiye aiki inda yawan kudinsu ya kama Naira miliyan 130.9.

A bangaren malaman makaranta kuma an samu ma’aikata 114 da suka bar aiki kuma gwamnati ta kashe Naira miliyan 196.8 wajen biyansu hakkokinsu.

Malam Hashim ya ce gwamnatin jihar tana biyan ’yan fansho kudadensu daga 1 zuwa 10 ga kowane wata maimakon a baya da ake biyansu a 10 ga wata zuwa karshen wata.

Ya gargadi ’yan fansho su guji bai wa kowa cin hanci idan suna neman hakkinsu kuma su taimaka musu wajen tona asirin duk  ma’aikacin hukumar fansho da ya bukaci su ba shi kudi.