✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 20 sun mutu a rikicin Musulmi da Hindu a Indiya

Ana ci gaba da zama cikin fargaba a Delhi, babban birnin Indiya bayan an kwashe tsawon lokaci ana rikici, inda rahotanni suka ce mabiya addinin…

Ana ci gaba da zama cikin fargaba a Delhi, babban birnin Indiya bayan an kwashe tsawon lokaci ana rikici, inda rahotanni suka ce mabiya addinin Hindu sun kona gidaje da shagunan Musulmi.

Bayanai sun ce, an kashe mutum 20 a rikicin da ake gani shi ne mafi muni da ya auku a babbarn birnin na Indiya cikin shekaru aru-aru.

Ranar Lahadi ce aka yi arangama a tsakanin masu zanga-zangar da ke goyon baya da masu adawa da wata dokar zama dan kasa wacce ake takaddama a kanta.

Amma sai rikicin ya rikide ya zama na addini, inda rahotanni suka ce wadansu na kai wa mutanen da ke bin addinin da ba nasu ba hari.

Hotuna da bidiyo da kuma rahotanni daga shafukan sada zumunta sun nuna yadda rikicin ya kazance, inda ’yan daba suke kai hari kan mutanen da ba sa dauke da makamai, ciki har da ’yan jarida; wadansu mutane dauke da adduna da sanduna sun kewaya hanyoyi da kuma mabiya addinin Hindu da ke kai hari kan Musulmi.

Ministan Birnin Delhi Arbind Kejriwal ya bayyana rikicin a matsayin “abin tayar da hankali” sannan ya yi kira “a kawo agajin sojoji.”

An fi kai hari a yankunan da Musulmi suka fi yawa, kamar su Maujpur da Mustafabad da Jaffrabad da kuma Shib Bihar da ke Arewa maso Gabashin Delhi.

Wakilin BBC, Faisal Mohammed ya ce titunan yankunan cike suke da duwatsu da fasassun gilasai da ababen hawan da aka kona da kuma warin hayaki da ya turnuke.