Da Dumi Dumi

Mutum 35 sun mutu a turmutsutsun jana’izar Kwamandan Iran

Jana'izar Kwamandan Iran

Rahotanni na bayyana cewa, a kalla mutum 35 ne suka mutu da raunata mutum 48 a yayin turmutsutsun da ‘yan kasar Iran suka yi don yin tururuwa zuwa wajen jana’izar babban kwamandan kasar Qassem Soleimani da aka kashe yayin wani hari da Amurka ta kai.

A rahoton da kafar sadarwar yanar gizo ta Young Journalists Club da talabijin, ta sanar da cewa kimanin mutum dubu 10 ne suka mamaye hanyar birnin Kerman da ke Iran, don halartar jana’izar Marigayi Qassem Soleimani da aka kashe ranar Juma’a.

Za a binne Qassem, ne a birnin Kerman bayan an dauki gawar daga cikin birnin Iran.

Kashe Qassem Soleimani da aka yi ya janyo fargabar yaki tsakanin Amurka da Iran, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

ADVERTISEMENT
Share