✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 38 sun mutu bayan kwalekwale ya kife da su a Bauchi

Mutum 38 suka mutu bayan wani kwalekwale ya kife da wasu manoma 40 a kogin Kirfi da ke Karamar Hukumar Kirfi jihar Bauchi. Shugaban Karamar…

Mutum 38 suka mutu bayan wani kwalekwale ya kife da wasu manoma 40 a kogin Kirfi da ke Karamar Hukumar Kirfi jihar Bauchi.

Shugaban Karamar Hukumar Kirfi Alhaji Bappa Danmalikin Bara, ne bayyanawa wakilinmu hakan lokacin da yake ganawa da manema labarai.

Alhaji Bappa, ya ce ”Ina mika sakon ta’aziyyata ga jama’ar Kirfi da jihar Bauchi game da rashin da rashin ’yan uwanmu da suka rasu a lokacin da suke hanyar su ta zuwa gona“.

Manoman su 40 sun shiga kwalekwalen yayin da kwalekwalen ya kife da su, mutum biyu daga cikin su ne kadai suka tsallake rijiya da baya, yayin da sauran suka nutse a cikin kogin.

Shugaban Karamar hukumar, ya kara da cewa, “Mun gano gawar mutuum biyu a hanyar garin Badara yayin da sauran ba a gano su ba zuwa yanzu, sai dai muna zargin duk sun mutu”, muna fatan Allah Ya gafarta masu.