Da Dumi Dumi

Mutum 500 sun kamu da coronavirus a masana’anta a Ghana

Gwajin cutar coronavirus

Hukumar Lafiya a kasar Ghana ta bayyana cewa sama da mutum 500 sun harbu da cutar coronavirus a wata masana’anta a kasar.

Ya zuwa yanzu wadanda suka harbu a kasar sun karu da kusan kashi 30 cikin 100 a cikin kwana daya.

Hukumar dai bata bayyana sunan masana’antar da aka samu hakan ba. A wani sako da ta fitar ta bayyana cewa a cikin ma’aikata  dubu daya da 300 mutum 533 aka tabbatar sun harbu da cutar.

A ranar Alhamis, kasar ta Ghana ta rawaito jimillar mutum  4,012 wadanda suka harbu da cutar a fadin kasar, inda 18 suka rasa rayukansu.

Hakan dai ya sanya kasar Ghana take kan gaba a yawan wadanda suka harbu da cutar a Yammacin Afirka. Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ne a rawaito cewa kasar ta Ghana ita ce kuma kan gaba a yawan gwaje-gwaje da aka gudanar a yankin game da annobar.

ADVERTISEMENT
Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya