✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum biyu sun kone kurmus a hadarin mota a Bauchi

Mutum biyu sun kone kurmus sannan mutane da dama sun samu munanan raunuka a kwani hadarin mota da ya auku an hanyar Bauchi zuwa Jos…

Mutum biyu sun kone kurmus sannan mutane da dama sun samu munanan raunuka a kwani hadarin mota da ya auku an hanyar Bauchi zuwa Jos a daidai kauyen Tashan Durumi da ke Karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi.

Hadarin ya auku ne kwana biyu bayan da wasu munanan hadarurruka biyu da suka jawo rasuwar mutum 17 a garin Bishi da ke hanyar zuwa Gombe a gabashin Bauchi da kuma Buzaye da ke yammacin Bauchi a hanyar zuwa Jos.

Kakakin Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) da ke Bauchi, Rilwanu Suleiman ya tabbatar da aukuwar hadarin, inda ya ce hadarin ya faru ne lokacin da wata motar dakon man fetur mai lamba BSA 664 DA ta yi taho-mu-gama da wata Toyota Hilud mai lamba FG 632 A15 na Ma’aikatar Albarkatun Ruwa ta Tarayya.

Rilwanu ya ce abin bakin ciki shi ne motar ta kama da wuta sai dai mutum biyu mace da namiji sun kone kurmus kuma an kai mutum uku da suka samu munanan raunuka Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, domin a yi musu jinya.