Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Mutum daya ya mutu, daya ya haukace a gasar shan kwayar da Kwastam ta kama

Shukaban Hukumar Kwastam na FOU shiyar A, Alhaji Muhammad Aliyu lokacin da yake duba aikin kona kwayar
Shukaban Hukumar Kwastam na FOU shiyar A, Alhaji Muhammad Aliyu lokacin da yake duba aikin kona kwayar

Wadansu matasa mazauna garin Sabo Shagamu sun bi dare inda suka yi ta lalibe a burbushin miyagun kwayoyin da Hukumar Kwastam da hadin gwiwar Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna (NAFDAC), suka kone a karkashin jagorancin Mataimakin Shugaban Hukumar Kwastam Alhaji Aminu Dahiru. Hukumomin biyu sun kone miyagun kwayoyin da Hukumar Kwastam ta kama ne da aka kiyasta kudinsu kan sama da Naira biliyan 14.                                                                                                                                                      Miyagun kwayoyin da suka hada da tiramadol da dangoginta cike a kwantaina 58 an yi aikin kone su cikin kwana biyu a dandalin kone kayayyaki irin wadannan a hanyar Ikorodu daga garin Shagamu a Jihar Ogun.

Aminiya ta samu labarin cewa, matasan mazauna garin Sabo Shagamu sun bi dare ne a ranar Juma’a suka yi ta lalube a burbushin miyagun kwayoyin suka kai ga wadanda ba su gama konewa ba suka yi ta jida suka tafi da su Shagamu suka yi gasar shan kwayar tiramadol.

ADVERTISEMENT

Malam Abdullahi Muhammad Alkwatanawi, mazaunin garin Shagamu ya shaida wa Aminiya  cewa matasan su uku ’yan ci-rani ne da suka zo garin Shagamu daga Arewa “Biyu daga cikinsu daga Jihar Sakkwato, yayin da gudan dan jihar Kebbi ne, daya daga cikinsu yana sayar da albasa ne, sai daya da ke sana’ar acaba, yayin da dayan yake sayar da lemo.”

Aminiya ta samu labarin cewa idan jami’an gwamnati suka kone kaya a wannan wuri matasa kan bi dare su je su yi laluben kayayyakin da aka kone, inda suke fakar idon ma’aikata su bi dare su tone kwayar da aka kone inda suka yi nasarar samun wadda ba ta kai ga konewa ba, sai su kwaso su shiga da ita Unguwar Sabo Shagamu, su sanya gasar shanta. “A wannan karo ma su kwaso kwayar suka yi gasar shan tiramadol ta hanyar zuba kwayoyin da dama a lemon kwalba suka yi ta dirka, inda suka yi ta yin ammanta yayin da daya daga cikinsu da bai yi aman ba ya mutu nan ta ke,” inji shi.

ADVERTISEMENT

Alhaji Ado Huntuwa wani dan kasuwa mazaunin Shagamu ya shaida wa Aminiya cewa, an yi jana’izar matashin da ya mutu a gasar shan tiramadol din da Kwastam ta kone a ranar Asabar da ta gabata. Ya ce, sunan marigayin Abubakar, kuma an yi masa Sallah a babban masalacin  Izala na garin Shagamu, “Kana daya daga cikin matasan da suka shiga gasar ya haukace ya fita daga hayyacinsa ana tunanin ya samu tabin hankali an garzaya da shi Arewa. Shi ma na ukun ba ya cikin hayyacinsa,” inji shi.

Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa, wadansu dillalan miyagun kwayoyin sun yi ta sayen  tiramadol da wadansu matasa suka yi kale a wajen da Hukumar Kwastam din ta kone su.

Wakilin Aminiya ya tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Ogun, DSP Abimbola Oyeyemi wanda ya ce ba ya da labarin faruwar lamarin domin zuwa lokacin ba a sanar da ’yan sanda ba.

Hukumar Kwastam ta sha alwashin yaki da sha ko safarar miyagun kwayoyi ta hanyar kamawa tare da kone miyagun kwayoyi a yankin.