Search
Subscribe
Mutum dubu 12 na neman cike gurbin aikin malamai dubu 2 a Jihar Sakkwato

Gwamnan-Jihar-Sakkwato Tambuwal

Mutum dubu 12 na neman cike gurbin aikin malamai dubu 2 a Jihar Sakkwato

Gwamnatin Jihar Sakkwato ta amince a dauki malaman makaranta 2,000, inda ta kafa kwamitin tantance masu nema karkashin jagorancin Farfesa Hamza Muhammad Maishanu Yabo.

Kwamitin ya kammala  aikin tantancewar a ranar Talatar da ta gabata bayan shafe fiye  da wata daya.

Kwamitin ya ce sama da mutum dubu 12 ne suka nuna sha’awar aikin na malanta, don haka za a  zubar da sama da mutum dubu 10 da ke neman aikin ke nan.

Aminiya ta zanta da Farfesa Hamza Muhammad Maishanu inda ya ce “Muna tantance wadanda suke da sha’awar aikin mun samu mutum sama da dubu 12 da suka kawo takardunsu a dukan kananan hukumomi 23 na Jihar Sakkwato, don Mai girma Gwamna ya ce mu yi adalci.”

Farfesa Maishanu ya ce suna da ka’idoji wajen tantancewa, “A tarbiyya da ilimi da girman sakamakon shaidar karatu da kuma iya rubutu da karatun mai son zama malami an tanadi maki 100, a haka ake raba su ta la’akari da dukan wadannan abubuwa da aka zayyana. Wanda bai samu nasara ba ya yi hakuri ya je wani wuri ya nema don gwamnati ba ta iya bai wa kowa aiki, za ta yi iyakar yin ta ne,” inji shi.

Farfesa Maishanu Yabo ya ce kananan hukumomin da suka fi yawan masu neman aiki sun hada da Tambuwal 1,500, Sakkwato ta Kudu da ta Arewa da Wamakko kowacensu mutum ya fi 1000, sai Yabo da take kusa da 1000.

Ya ce harkar karantarwa aba ce da ya kamata a yi taka-tsantsan  don samun nasara , inda ya ce ana son jajircewa da nuna kwazo da bayar da tarbiyya ga wadanda suke karkashin malaman.

Aminiya ta lura alfarma ta dabaibaye aikin daukar malamai, abin da ke kai wadansu masu neman aikin sun saba wa dokokin da aka gindaya kuma su tsallake siradi saboda dangantakarsu da masu daukar aikin ko da wani jigo a gwamnatin jihar.

Wakilinmu ya ji ta bakin wani da ya zo yin tantancewar ya ce “Na zo ne kawai don nema mutum ba ya bari sai ya samu, amma in ka dubi tarin mutanen d ake zuwa wajen neman aikin da wadanda ake zuwa da su ba su bin layi a je a yi musu su wuce ka san dai mu talakawa sai dai in Allah Ya ce sai mun samu ne kawai za mu samu amma wannan mutum 2000 da za a dauka ko a bangaren manya da masu neman alfarma za su kare. Ni dai na bar wa Allah komai.”

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin