Da Dumi Dumi

Mutum miliyan 500 ke yin ayyukan da ba so a duniya

Sabuwar kididdigar da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar, ta nuna kusan mutum miliyan 500 ne ke yin ayyukan da ba sa muradi, ko ma ba sa so sam.

Hukumar Kwadago Ta Duniya ta ce rashin aikin yi ga al’umma zai karu da miliyan 2,500,00 a wannan shekara, sakamakon tattalin arzikin duniya da ya kasa tsayawa da kafafunsa, kamar yadda BBC ya ruwaito.

Hukumomin sun yi amanna wannan abin damuwa da dubawa ne, a daidai lokacin da takardun neman aiki suka cika masana’antu da ma’aikatu da sauran wurare.

Hukumar kwadagon ta ce matsalar rashin daidaito tsakanin maza da mata a wuraren ayyuka, da ratar shekaru, da ainahin inda ayyukan suke duk abin damuwa ne.

An kuma samu karuwar zanga-zanga, da yajin aikin a kasashen duniya tsakanin shekarun 2009 da 2019.

ADVERTISEMENT
Share