Search
Subscribe
Mutum miliyan daya suka kalli bidiyon wakar Jaruma a mako uku

Mutum miliyan daya suka kalli bidiyon wakar Jaruma a mako uku

Wakar fitaccen mawakin Hausa da ke jan zarensa yanzu a cikin mawaka, wato Hamisu Breaker ta Jarumar Mata tana tashe sosai a kafofin sadarwa.

Wakar wadda mawakin ya saka a mako uku da suka gabata, ta samu mutum miliyan daya da suka kalla a kafar YouTube kawai a cikin mako uku, wanda ba kasafai ake samun irin hakan ba a wakokin Hausa.

Da yake bayyana jin dadinsa kan lamarin, ya wallafa a shafinsa na Instagram cewa, “Alhamdulillah Mutum miliyan 1 sun kalli wakar Jaruma a mako uku. Na gode sosai masoyana.”

Ita dai wakar Jaruma ta yi fice sosai ne musamman bayan da aka yi gasar #DanceForHusband a lokacin sallah, inda mata suka rika sanya wakar suna rawa a gaban mazajensu, lamarin da ya tayar da kura.

Hamisu Sa’id, wato Breaker mawaki ne da ya fara fice da wakarsa ta Shimfidar Fuska, inda tun daga lokacin yake ta sakin sabbin wakoki.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin