✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum uku sun gurfana a gaban kotu kan jingina Kwamishina da APC a Gombe

An gurfanar da wasu mutum uku masu suna John Dabid da Ishiaku Yusuf da Gad Lashuru da suke zaune a Abuja da Baganjen billiri a…

An gurfanar da wasu mutum uku masu suna John Dabid da Ishiaku Yusuf da Gad Lashuru da suke zaune a Abuja da Baganjen billiri a Jihar Gombe a gaban Kotun Lardi ta 3 da ke garin Gombe, bisa tuhumarsu da laifin hada baki da yin karya tare da buga foster wani kwamishina suna likawa a ranar 23 ga Fabrairun bana.
Wadanda ake zargin sun buga fosta dauke da hoto da sunan Kwamishinan Sufuri da Gidaje na Jihar Gombe Mista Rabenson Zabulum Wasa da alamar Jam’iyyar APC suka bi suna lillikawa a jikin gini a garin Baganjen billiri don su bata masa suna saboda sun san shi dan Jam’iyyar PDP ne kuma Kwamishina.
dan sanda mai gabatar da kara Sufeto Bako Gadam, ya shaida wa kotun cewa aikata haka laifi ne da ya saba wa sassa na 97 (1) da 391 (1) da kuma 394 na kundin laifuffuka da hukuncinsu (Penal Code).
Wadanda ake tuhumar sun ki amincewa da zargin, inda suka ce idan aka matsa musu za su fasa kwai, inda nan take lauyansu Barista Luka A. Haruna ya yi amfani da sassa na 341 (2) da 36 (5) ya roki kotu da ta ba da belinsu.
Alkalin kotun Barista Ahmad Baba Bala, ya amince da rokon lauyan, inda ya ba da belinsu kan wasu sharudda, sannan ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar Talata mai zuwa don fara sauraron shaidu.