Da Dumi Dumi

Mutum zai iya duk wata hidima da sana’ar gyaran takalmi –Adamu Dan Kwada

Malam Adamu Nuhu ‘Xan Kwada a bakin sana’arsa
Malam Adamu Nuhu ‘Xan Kwada a bakin sana’arsa

Malam Adamu Nuhu Dan Kwada mai sana’ar gyaran takalmi a jikin tsohon Masallacin Juma’a na Tudun Jukun Zariya, wanda ya ce, ya kwashe shekara 35 yana sana’ar ya ce, akwai rufin asiri a cikinta matukar mutum ya tsare gaskiya. Ya shaida wa Aminiya cewa da ita ya yi aure ya gina gida ya sayi gona ya kuma aurar da kannensa uku:

Shekara nawa ka yi kana sana’ar gyran takalmi?

Adamu Dan Kwada: Zan kai shekara 35 da fara wannan sana’a. A farko ina yawo ne da akwatina unguwa-unguwa domin neman gyaran takalma ko gyaran jaka da sauransu. A garin Zariya kusan babu unguwar da ban shiga ba da wannan sana’a tawa ta gyaran takalmi a shekarun baya kafin in fara zama wuri daya.

Koyon sana’ar ka yi?

Adamu Dan Kwada: Eh na koya ne wajen dan uwana a lokacin shi ya fara fita ci-rani, to idan ya dawo gida nan kauyen Faruruwa a garin Dan-Kwada da ke Karamar Hukumar Shanono a Jihar Kano, sai in rika koyo har Allah Ya sa na iya, kuma daga nan  na fara biyo shi garin Zariya ci-rani tare da sana’ar, tun tsawon wancan lokaci har zuwa yau.

ADVERTISEMENT

To sana’ar dukanci da sana’ar gyaran takalmi akwai bambanci ne ko duk daya ne?

Adamu Dan Kwada: Akwai bambanci saboda dukanci ta shafi kamar dinkin layu da yin gidan takwabi da duk wani abu da ake yi wa ado da fata, sai kuma  sa hancin takalma kawai. Amma sana’ar gyaran takalmi (shushaina) ya shafi zamani ne. Kamar dinka sabon takalmi, dinka bel da yin rawul na takalma da gyaran akwatunan zamani, kai a yanzu har gyaran  bokatan da ake yi da roba na zuba ruwa muke yi domin mun fi masu gyara na wuta iyawa kuma namu ya fi kyau don haka gyaran takalmi (shushaina) ya shafi gyara irin na zamani ne.

Ka san kowace sana’a akwai dadinta, akwai rashin dadinta kai wane bayani za ka yi a kai?

Adamu Dan Kwada: To ni dai na gode wa Allah domin wannan sana’a tawa ta gyaran takalmi na ji dadinta kuma ina kan jin dadinta. Ta biya min bukatu da daman gaske. Na farko na yi aure na gina gida irin namu na kauye, kuma na sayi gona tun duniya na kwance a kan Naira 550 wadda a yanzu ba zan sayar da ita Naira dubu 200 ba, kuma na yi wa kannena aure, na biya wa dana kudin makarantar kwana a garin Gwarzo da ke Kano.

To yanzu misali a wannan sana’ar a rana daya kana iya samun nawa?

Adamu Dan Kwada: To shi samu ya danganta ne wani lokaci za ka iya samun Naira dubu wani lokaci har dubu 2, wani lokaci kuma sai dai na abinci za ka samu, don haka ka ga da wuya in iya yin aikin albashi da za a biya ni Naira dubu 30 a wata. Don haka ba zan iya karin kasuwanci ba sai dai idan babban jari ne a harkar a gaskiya ba zan iya ba.

Wadansu na ganin sana’ar gyaran takalmi ba ta da muhimmanci sosai har wani shugaba ya taba ba da misali cewa har ma za ka ga dan shushaina ya auri mata hudu yaya ka ji da irin wannan furuci?

Adamu Dan Kwada: To ai wannan rashin sanin sirrin sana’ar ce, ya sa ya fadi haka. Domin ni yanzu ai ka ji na fada maka irin yadda nake ji a cikin sana’ar da hidimar da nake yi. Kuma ai ka ga shi auren mata da yawa ra’ayi ne ni komai mukamina ba zan iya aje mata fiye da biyu ba.

To yanzu matanka nawa?

Adamu Dan Kwada: Matata daya kuma ina da ’ya’ya 7 na aurar da mace sannan babban dana wanda na ce maka ya yi karatu a makarantar Gwarzo shi ma ya yi aure, kuma ka gan ni idan na zo Zariya na samu kamar wata daya ina sana’ata sai kuma in je gida can kauye in duba iyalaina. Idan da damina ce sai in yi kamar mako biyu a gida ina noma in kuwa da rani ne duk inda na yi mako daya sai in dawo Zariya wajen sana’ata in ci gaba da nema, tunda nan inda nake kamar gida ne a wurina, kuma jama’a sun saba da ni domin daga wurare za ka ga ana kawo min gyara har nan inda nake ba tare da na je wani wuri ba.

To wane kira za ka yi ga jama’a?

Adamu Dan Kwada: To ina kira ga al’umma da su zamo masu hakuri a kan sana’arsu su kuma rike gaskiya a ko’ina suke da yin hakuri Allah zai taimake su domin Allah Yana tare da mai hakuri da kuma mai gaskiya.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya