✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutumin da ya shuka bishiyoyi sama da miliyan 5 don kaucewa zaizayar kasa ya rasu

Wani dattijo mai suna Bishweshwar Dutt Saklani mai shekara 96 ya rasu ranar 18 ga Janairu 2019, da ke unguwar Pujargaon a jihar Uttarakhan ta…

Wani dattijo mai suna Bishweshwar Dutt Saklani mai shekara 96 ya rasu ranar 18 ga Janairu 2019, da ke unguwar Pujargaon a jihar Uttarakhan ta kasar Indiya, tarihi ba zai taba mantawa da wannan mutum ba da ake yi wa lakabi da suna “Tree Man of Uttarakhan” wato mutum mai sha’awar shuka bishiyoyi.

Bishweshwar, ya sadaukar da rayuwarsa akan abin da yake sha`awa inda ya shuka sama da bishiyoyi miliyan 50 a dajin jihar Uttarakhan.

Bishweshwar, ya kasance mai sha’awar bishiyoyi a rayuwarsa, ya fara shuka bishiya ta farko ne tun yana dan shekara takwas lokacin da yake tare da kanin mahaifinsa, wanda ya kasance yana lura da shi har zuwa lokacin da ya kai shekara 70 daga nan tsufa ya kama shi ya makance, daga bisani Bishweshwar ya maida dajin garin Pujargaon gidansa.

Sha`awar da Bishweshwar ke yi wa bishiyoyi sananniya ce a garin, saboda wani lokacin ya kan kira bishiyoyi a matsayin `ya `yansa ko kuma  abin da ya fi kusanta, wasu masana muhalli na cewa, shuka bishiyoyi na iya magance zaizayar kasa ko magance gurbatar muhalli, wanda Bishweshwar na taimaka wa rayuwar jama`ar garin.

`Yan uwan Bishweshwar sun ce, a lokacin da dan uwan Bishweshwar, mai suna Nagendra Dutt Saklani, daya daga cikin shugaban tsarin burguzu na yankin wanda tun bayan rasuwarsa, Bishweshwar ya fara shiga daji tun safe ya wuni yana dasa bishiyoyi. A shekarar 1958 matarsa ta farko ta rasu, daga nan ya kara lokutan da yake yi a dajin yana dasa bishiyoyin a cewarsa hakan zai rage masa radadin rashin matarsa. Wannan na nuna cewa, ya sadaukar da rayuwarsa akan rasuwar dan uwansa da matarsa.

An dai kiyasta Bishweshwar ya shuka sama da bishiyoyi miliyan 5 nau’uka daban-daban na tsirrai, jama`ar garin sun kasance su na sha`awar ayyukan da yake yi masu, yayin da farko jama`ar garin na kushe hidimar da yake yi masu wani lokacin har dukansa suke yi saboda su na ganin yana yin ayyukan da ba gurbinsa ba ne, duk da haka bai mika wuya akan tsangwamar da ake yi masa ba. Ya ci gaba da shuka bishiyoyin saboda sha`awar da yake yi na shuke-shuken, kotun garin ta tabbatar da shuka bishiya ba laifi ba ne.

Bishweshwar ya fadada dajin garin a cikin shekara 10 na bara, ya makance kafin ya rasu, ya shuka bishiyoyi sama da miliyan 5 a kadada 120.